Most Reverend Dakta Daniel Okoh, shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa ne ya jaddada wannan bukatar a yayin da yake jawabinsa a taron majalisar Kiristoci ta Najeriya CCN da aka kammala a Inugu, babban birnin jihar Inugu yau Asabar .
Ya ce, “Dole ne mu nuna tausayawa ga mabukata, musamman masu rauni, kamar masu nakasa. Dole ne Ikilisiya a tabbatar an shigo da masu nakasa cikin ayyukan Ikilisiya. Suna da baiwa kamar yadda sauran mu ke da baiwa, kuma suna da gudummawar da zasu kawo ga ci gaban Ikilisiya da al’umma. Mu basu dama su mamaye gurin da ya dace a c cikin Ikilisiya da kuma a cikin al’umma.”
Shugaban kungiyar Kiristocin dai ya kara da cewa lokaci ya yi da Ikilisiya zata kara yunkuri wajen yin cudanya da Musulmai a fannin tattaunawa tssakanin addinai a kowane mataki.
Ya kuma ce, “Yanzu lokaci ne na kara kokari don hana kalaman kiyayya masu tsananta yanayin da ke wanzuwa tsakanin mabiya mabanbantan addinai a kasar mu. Gaskiya ita ce bamu da wani zabi, saboda muna rayuwa ne tare a wannan kasa ta Najeriya, kuma dole ne mu nemo hanyar da zamu kasance tare cikin kwanciyar hankali da lumana.”
Shi kuwa shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kaduna, Reverend Joseph John Hayab ya ce, “Gaskiyar ita ce, mun gane cewa a addinance bamu yi wa nakasassu da kyau ba. Abin da CAN take so a ga an yi shine Ikilisiya ta zama gidan kowa da kowa, da nakasassu da masu lafiya, domin Allah yana kaunar kowa."
Hayab ya ce "Bari mu san cewa suna da gudummawar da zasu kawo. Saboda haka, ya kamata mu kalle su da daraja, don su ma su kawo tasu gudummawa wajen ci gaban addini da rayuwa. Idan bamu yi haka ba, toh ba mu yi abin da addini ya koya mana ba.”
Saurari cikakken rahoton Alphonsus Okoroigwe: cikin sauti: