Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar CAN Ta Tabbatar Da Cewa ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 57


Kuniyar Kiristoci ta Najeriya CAN
Kuniyar Kiristoci ta Najeriya CAN

Kungiyar Kiristan Najeriya, CAN, reshen Jihar Kaduna ta ce duk da ikirarin nasara kan 'yan-bindiga da gwamnati ta yi, har yanzu akwai matsalar tsaro a wasu yankunan Jihar Kaduna saboda ko a Larabar da ta gabata 'yan-bindigan sun sace wasu mutane 57 a wani  yanki na karamar hukumar Kajuru.

KADUNA, NIGERIA - Cikin 'yan-kwanakin da su ka gabata dai hare-haren 'yan-bindiga sun yi sauki a sassan Jihar Kaduna har ma gwamna Nasuru Ahmed El-Rufa'i na bada tabbacin ci gaba da walwalar al'umma saboda nasarorin da jami'an tsaro ke samu kan 'yan-bindiga a wasu yankuna na Jihar. To sai dai shugaban kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN, reshen jahar Kaduna, Rabaren John Joseph Hayab ya ce har yanzu akwai saura rina a kaba game da matsalar tsaro.

Rabaren Hayab ya ce wasu mabiya na cikin ibada a yankin Kurmin Juwa dake karamar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, kawai sai 'yan-bindiga su ka afka musu, inda su ka sace mutane 57, amma kuma mutane 14 sun samu tsira, yanzu saura mutane 43 a hannun 'yan-bindigan, kuma har sun fara maganar kudin fansa.

‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga

Dama dai gwamna Nasuru Ahmed El-Rufa'i ya ce duk da nasarar da aka yi kan 'yan-bindigan wasu sun sauya mafaka, ko da ya ke dai gwamnan ya ce ko ina 'yan-bindigan su ka shiga ma, za a gama da su.

Masani kan harkokin tsaro Manjo Muhammadu Bashir Shu'aibu Galma mai ritaya ya ce dama duk dabi'ar 'yan-bindiga ce su rinka kai hare-haren don nuna gazawar gwamnati.

Manjo Galma ya ce yanzu ya ragewa jami'an tsaron ne su maida hankali wajen ganin sun farwa 'yan-bindigan a sabbin guraren da su ka fara kai hare-haren baki daya.

Kimanin wata guda kenan da samun saukin hare-haren 'yan-bindiga a Jihar Kaduna sakamakon sauya salon aikin jami'an tsaro ta yadda su ka fara bin 'yan-bindiga har daji su na murkushe su, amma hare-haren kwananan a yankin kudancin Kaduna da kuma Birnin Gwari na neman maida hannun agogo baya.

Saurari cikakken rahoton daga Isah Lawal Ikara:

Kungiyar Kiristoci Ta Kasa CAN Ta Tabbatar Da Cewa ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 57.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

XS
SM
MD
LG