A yayin da 'yan Najeriya ke hutun Mauludi a Litinin din nan, bukukuwan Mauludi a jihar Kaduna ya sami halartar malam addinin Kiristoci da shugabanni daban-daban.
Taron murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Sallallahu alaihiwasallam na bana dai ya maida hankali ne akan addu'o'in neman zaman lafiya da kuma kaunar juna, kuma mataimakin shugaban kungiyar Fitiyanu, Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaria shine shugaban taron na bana a jahar Kaduna, kuma ya nunar da bukatar kaunar juna tsakanin al'umomi daban-daban.
Manyan malaman addinin Kirista da dama ne su ka halarci taron Mauludin na bana kuma mai baiwa gwamna shawara kan harkokin addini Sheikh Auwal Assudany ya ce hakan na da fa'ida matuka.
Assudany ya ce da ma Kiristoci kan halarci taron Mauludin amma na bana an kara samun cigaba inda ya nunar da yuwuwar kara samun cigaba da tsaro ta hanyar irin wannan hadin kai tsakanin Musulmi da Kiristoci.
Pastor Yohanna Buru wanda ya jagoranchi Kiristocin da su halarci Mauludin ya ce wannan tushe ne na magance matsalolin tsaro. Buru ya ce idan dai aka hada kai tsakanin Musulmi da Kirista to duniya za ta zauna lafiya.
Shugaban matasan Darikar Tijjaniya na Afirka, malam Ahmed Tijjani Umar ya nuna muhimmancin bikin Mauludin da ya ce ya na bada damar addu'o'in magance matsalolin dake damun kasa.
Saurari cikekken rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna: