Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Bude Iyakokin Kasar Nijar


Wasu jeri dogayen motocin dakon kaya.
Wasu jeri dogayen motocin dakon kaya.

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun bada sanarwar sake bude iyakokin kasar da nufin baiwa jama’a damar zirga-zirga a tsakanin kasar da kasashe makwafta amma da sharadin nuna takardar shaidar gwajin cutar COVID-19.

Taron majalisar ministocin da aka yi a ranar Alhamis ne ya yanke shawarar sake bude iyakokin kasa bayan wata tattaunawar da aka yi a kwanakin baya tsakanin shugabanin kasashen Afirka ta yamma da mambobin kungiyar UEMOA.

A watan Afrilun 2020 ne gwamnatin Nijar ta bada sanarwar rufe iyakokin kasa da na sama sanadiyar annobar coronavirus kafin daga bisani a sake bude filayen jiragen sama da sharadin kowane fasinja ya nuna takardar gwajin wannan cuta.

Makamancin wannan sharadi ne gwamnatocin kasashen na Afrika ta Yamma renon Faransa suka gindaya wa fasinjojin da ke shirin ketara iyakokin kasa wato gabatar da takardar gwajin cutar COVID-19 ya zama wajibi akan iyakokinta.

Kamfonin sufuri sun yi na’amda wannan mataki wanda tuni da ya fara farfado da harkoki kamar yadda yanzu aka fara yin lodin farko daga kamfanin STM Transports zuwa Cotonou a Jamhuriyyar Benin in ji wani kakakin kamfanin Mahaman Inchourout.

Kafin rufe iyakokin kasa a bara, motocin jigilar kamfanonin sufuri daban-daban kan tashi daga birnin Yamai shake da lodin fasinjoji a kowace rana zuwa biranen Cotonou, Lome, Accra, Abidjan, Ouagadougou da Bamako kamar yadda irin wadanan motoci kan tasowa daga wadanan birane kuma zuwa birnin na Yamai dauke da ‘yan kasuwa.

Saboda haka matakin sake bude iyakokin kasawani abu ne da zai farfado da hada-hada a tsakanin kasashen Yammacin Afrika wadanda su ma kamar sauran sassan duniya suka dandani kudar annobar coronavirus.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

An Sake Bude Iyakokin Kasar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00


XS
SM
MD
LG