A Jamhuriyar Nijar, wani shirin gina otel domin ‘yan majalisar dokokin kasa ya haifar da ce-ce-kuce dangane da yawan kudaden da za a kashe wajen gudanar da wannan aiki.
A watan mayun da ya gabata ne aka yi rajistar kwangilar ginin sabon hotel din da za ta zamewa ‘yan majalisar dokokin kasa masauki a tsawon lokutan da za su shafe na halartar zaman majalisar dake nan Yamai.
Sai dai tuni wasu ‘yan Nijar suka yi wa wannan yunkuri ca saboda a cewarsu, bukatun al’uma a yau sun wuce batun gina otel. Alhaji Salissou Amadou mamba ne a kungiyar RNDD.
“Tsakani da Allah wai babu abin da za a rika yin lissafi daidai da rayuwar talaka, wannan abu a tsakani da Allah an yi talaka adalci” In ji Amadou.
Da yake mayar da martani ga masu korafi akan wannan aiki dan majalisar dokokin kasa Hon. Lawali Ibrahim Mai Jirgi na cewa, bai ga laifi bai idan aka saka ‘yan majalisa cikin kyakkyawan yanayin aiki.
Sama da million 14,000 na cfa ne aka bayyana cewa za a kashe ta hanyar wannan kwangila da aka baiwa wani kamfanin cikin gida nauyin aiwatar da shi, abin da ‘yan rajin kare hakkin jama’a ke ganin tamkar almubazaranci ne aka yi da kudin kasa.
Tun a shekarar 2012 ne majalisar dokokin kasa ta bullo da shawarar ginawa ‘yan majalisa otel don maye gurbin dakunan da suka saba sauka.
Sai dai hakan ba ta samu ba har zuwa lokacin da shudadiyar majaliar da Ousseini Tinni ya jagoranta ta farfado da wannnn aiki.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma: