Rashin bayar da cikakun bayanai daga wajen hukumomi a wannan lokaci da shirye-shiryen aikin shimfida bututun mai ke kankama ya sa kungiyar ROTAB fitar da sanarwa da nufin jan hankalin mahukuntan Nijar a game da batun rajistar mutnanen da wannan aiki zai ta da daga matsugunansu.
Da jin wannan korafi ma’aikatar ministan man fetur ta kira wani taron da ya hada jami’anta da na kungiyar ROTAB inda suka tattauna wannan batu.
Yunkurin jin ta bakin jami’ai a ma’aikatar man fetur bai yi nasara ba to amma da yake bayani a game da batun rajistar mutanen da bututun mai zai ratsa matsugunansu a karamar hukumar Ourafane ta jihar Maradi magajin garin na Ourafane Malan Nafiou Habou ya ce ayyukan rajistar na gudana ba tare da wata tangarda ba yayin da kuma ake ci gaba da ayyukan wayar da al’uma.
Kananan hukumomi kimanin 33 na Jihohin Diffa da Zinder da Maradi da Tahoua da Dosso ne bututun man da za a shimfida a tsawon km 1,298 zai ratsa kafin ya shiga Jamhuriyar Benin inda zai keta km 694 akan hanyarsa ta zuwa gabar teku.
A watan Satumban2019 ne tsohon shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ya dasa tubalin farko na soma ayyukan shimfida wannan bututu da zimmar samar da hanyoyin fitar man kasar zuwa kasuwannin duniya .
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: