Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Zabe Ta Kori Karar Atiku Kan Zargin Tinubu Da Mallakar Takardun Kasashe Biyu


Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

Kotun har ila yau ta yi watsi da zargin mika wasu kudade da aka ce Tinubu ya yi ga hukumomin jihar Illinois a Amurka, wadanda ake alakantawa da na safarar muggan kwayoyi.

Kotun da ke sauraron kararrakin zabe a Najeriya ta yi watsi da karar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya shigar a gaban kotun don kalubalantar nasarar jam'iyyar APC a zaben.

Atiku ya kalubalanci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na APC kan cewa Tinubu ya mallaki shaidar da ke nuna cewa shi dan Najeriya ne kuma dan kasar Guinea.

A cewar Atiku, a dalilin haka, bai kamata Tinubu ya tsaya takarar shugaban kasa a Najeriya ba.

Sai dai yayin da kotun ta sauraron kararrakin zabe take gabatar da hukunce-hukuncenta a ranar Laraba a Abuja, Alkali Moses Ugo, ya ce wannan wani sabon batu ne cikin kararrakin da PDP ta shigar.

A cewar Alkali Ugo, batun ba ya cikin asalin korafe-korafen da Atiku ya shigar tun farkon shigar da karar.

A wani hukunci da ta yanke har ila yau, kotun ta kori karar da Atikun ya shigar kan cewa Tinubu ya taba mika wasu kudade da yawansu ya kai dala 460,000 ga hukumomin jihar Illinois a Amurka bayan cimma matsaya dangane da wata shari’a da ake tuhumar Tinubun kan mallakar muggan kwayoyi.

A zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, hukumar zaben Najeriya ta INEC ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hakan ya sa Atiku da jam’iyyarsa ta PDP da Peter Obi da jam’iyyarsa ta LP, suka shigar da kararraki a gaban kotun da ke sauraron kararrakin zaben.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG