ABUJA, NIGERIA - A cewar Festus Keyamo, mai magana da yawun yakin neman zaben Tinubu, zababben shugaban kasan ya isa ne a ranar 26 ga Afrilu, 2023, kuma zai rika karbar bayanan tsaro a kullum yayin da kuma yake shiri domin ranar rantsar da shi.
Yunkurin da Tinubu ya yi zuwa Abuja ya biyo bayan dawowar sa ne daga hutun da ya yi a Landan da Paris, inda ya shafe sama da wata guda. Rashin bayyanarsa da karancin fitowar sa a bainar jama'a a lokacin da yake tafiyar ya sanya damuwa kan lafiyarsa da kuma yadda zai iya biyan bukatun fadar shugaban kasa idan ya karbi mulki.
Sai dai a wani dan takaitaccen jawabi da yayi ranar da ya dawo 24 ga watan Afrilu, Tinubu ya tabbatar wa magoya bayansa cewa ya dace kuma a shirye yake ya fara aiki.
Tinubu ya fito ne a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, inda ya doke Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP), da wasu ‘yan takara 15 a zaben da aka fafata.
Obi da Atiku sun gabatar da koke daban-daban ga kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, inda suka bukaci a bayyana su a matsayin wadanda suka lashe zabe na gaskiya ko kuma a sake sabon zabe saboda zargin tafka magudi.
Kungiyoyin Action Alliance (AA), Allied People's Movement (APM), da Action People's Party (APP) suma sun gabatar da koke-koke na soke zaben.
Sai dai kuma ana shirin rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu, kafin a kai ga kammala karar a kotun koli a watan Oktoba.
Sai dai Masana na ganin cewa ya kamata a lura babu wani shugaban Najeriya mai ci da kotu ta taba tsige shi.