Labarin zantawar sakataren Harkokin wajen Amurka Antony Blinken da zababben shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ta wayar tarho ta girgiza dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.
Dama dai tun a ranar Laraba ne ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da cewa Blinken ya gana da Tinubu a game da batutuwan da suka shafi dangantakar Najeriya da Amurka yayin da kasar ta ke ci gaba da shirye-shiryen tarbar sabon gwamnatin kasar.
“Ina cike da mamakin cewa @Blinken ya kira Tinubu ta wayar tarho, sabanin matsayar da Amurka ta bayyana karara agame da zaben shugaban kasar Najeriya na 2023”.
“Hankali ma ba zai dauki wannan al’amari ba, cewa Amurka, wace ta kasance tushen Demokradiyya, ta amince da wannan abun yaudarar da aka yi da sunan zabe a ranar 25 ga watan Fabrairu.”
Halasta zaben da dama aka amince cewa an tafka magudi a ciki, wani al’amari ne da zai iya yi wa ‘yan kasar wadanda suka jajirce akan tabbatar da demokradiyya da kuma sahihancin akwatin zabe kasa a gwiwa k@StateDept @POTUS @USinNigeria. – a cewar Atiku Abubakar.
Idan ba a manta ba, da safiyar jiya ne Tunde Rahman, mai Magana da yawun zababen shugaban kasar na Najeriya ya bada sanarwar cewa “Sakataren harkokin wajen Amurka Antony J. Blinken ya maganta da safiyar yau (jiya Talata Kenan) da shugaban Najeriya mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu domin jaddada wa sabon gwamnati mai shigowa goyon bayanmu na cigaba da karfafa dangantaka tsakanin Amurka da Najeriya”.