Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Filato Ya Ce Kotun Daukaka Kara Ba Ta Yi Masa Adalci Ba


Gwamnan Jihar FIlato Caleb Mutfwang
Gwamnan Jihar FIlato Caleb Mutfwang

Gwamnan jihar Filato, Caleb Manasseh Mutfwang, ya shaidawa kotun koli jiya cewa, kotun daukaka kara ba ta yi masa adalci ba wajen soke zabensa.

WASHINGTON, D. C. - Mutfwang, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar wa kotun kolin batutuwa takwas da ya gabatar wa kotun daukaka kara domin tabbatar da sahihancin zabensa, da yace daga ciki, daya ne kawai aka tantance, ya kuma ce kotun daukaka kara ba ta yi masa adalci ba.

Ya bukaci kotun koli da ta ayyana shi a matsayin zababben gwamnan jihar Filato.

Mutfwang, wanda ya bayyana hakan a cikin takaitaccen bayaninsa a kotun koli mai membobitakwas na manyan lauyoyin Najeriya karkashin jagorancin Kanu Agabi, ya ce "doka a bayyane take cewa, duk inda aka yi kuskure, akwai hanyar gyara."

A ranar Talata ne ake sa ran za a saurari takaitaccen bayanin sa a kotun koli. Ya ce: “An hada batutuwa takwas kuma an gabatar da su a gaban kotun da ke kasa domin tantancewa, amma abin takaici, batu guda daya ne kawai (na shari'a) kotun ta daukaka, ta yanke shawarar barin batutuwa bakwai da ba a taba su ba.”

“Wannan kotu ta bayyana a lokuta da dama cewa, ya kamata kotunan tsaka-tsaki su bayyana dukkan batutuwan da aka gabatar a gabansu. Kada ta tsaida shi kan wani batu daya ko ra'ayi a yi watsi da sauran batutuwa.

Mutfwang ya dage cewa tun da ba a yi masa adalci a kotun daukaka kara ba, ya kamata kotun koli ta yi watsi da hukuncin na kotun daukaka kara na soke zabensa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG