Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Najeriya Za Ta Saurari Karar Gwamnan Jihar Kano A Ranar Alhamis


Nasiru Yusuf Gawuna da Abba Kabir Yusuf
Nasiru Yusuf Gawuna da Abba Kabir Yusuf

Hankali ya koma kotun kolin Najeriya a jajiberin sauraron daukaka karar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, kan kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da ya soke zaben sa tare da bai wa abokin hamayyar sa Nasiru Yusuf Gawuna nasara.

A ranar Alhamis kotun koli za ta yi zaman sauraren karar, inda za ta duba bangaren da ke kan daidai a dambarwar.

Kasanacewar lamari ne na kotu, masu ruwa da tsaki na bangarorin biyu na takatsantsan wajen ayyana nasara, amma wasu magoya baya na gefe da ba sa shakkar hukuncin kotu, su na fadar abin da zai karfafawa sauran magoya baya guiwa.

Yawan kuri'un Kano da tasirin jihar a zaben shugaban kasa ya sa ake maida hankali kan ta, musamman a yayin da mulki ya koma hannun 'yan hamayya, sakamakon tasirin magoya bayan tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso.

Koma yaya shari'ar za ta kaya, duk bangaren da ya sami nasara a karshe zai kara karfi akalla dai na tsawon shekaru hudu zuwa wani zagayen babban zabe a 2027.

Gabanin yanke wannan hukuncin, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi zama da shugabannin jam'iyyun NNPP da na APC a Kano, inda suka rattaba hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Yanzu dai an zuba ido a ga yadda bangarorin biyu za su girmama wannan yarjejeniya ta zaman lafiya domin kiyaye duk wani tashin hankali ko ta da tarzoma bayan yanke hukunci, wanda daga shi babu wani.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG