Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masar Ta Gabatar Da Wani Tsari Na Kawo Karshen Yakin Gaza


Diaa Rashwan - Shugaban Hukumar Yada Labaran Kasar Masar
Diaa Rashwan - Shugaban Hukumar Yada Labaran Kasar Masar

Masar ta ba da tabbaci a ranar Alhamis cewa ta bullo da wani tsari da zai iya kawo karshen rikicin da ke tsakanin Isra'ila da Hamas a Zirin Gaza wanda ya kunshi matakai uku da za su kai ga cimma matsayar dakatar da bude wuta, tana mai cewa yanzu tana jiran a ba ta amsa kan wannan bukata da ta mika.

WASHINGTON, D. C. - Shugabar Hukumar Yada Labarai ta Masar, Diaa Rashwan, ya fada cikin wata sanarwa da ya fitar cewa Masar za ta ba da cikakkun bayanai kan shirin da zarar an samu amsar tsara da ta mika.

Shirin wani yunkuri ne kunshe da shawarwari "na gayyato dukkan masu ruwa da tsaki kan teburin sasantawa a wani mataki na dakatar da zubar da jinin Falasɗinawa da hare-haren da ake kai wa Zirin Gaza da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin," in ji shi.

A baya, majiyoyin tsaron Masar sun ce shawarar ta hada da dakatar da bude wuta, da matakai da dama da suka hada da sakin fursunonin Isra'ila da Hamas. Wata majiyar Masar ta ce an taso da manufar kafa gwamnatin da za ta rike yankin na Gaza bayan yakin.

Har yanzu Masar ba ta samu amsa kan shawarar bangarorin da abin ya shafa ba, kuma za ta ba da cikakken bayani game da abin da shirin ya kunsa da zarar an samu wadannan martani, in ji Diaa Rashwan, shugaban hukumar yada labaran kasar Masar.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG