WASHINGTON, D. C. - Arouri babban jami'i ne a tsarin shugabancin kungiyar ta Hamas, kuma daya daga cikin wadanda suka kafa reshen soji na kungiyar dakarun Qassam Brigades, wadanda suka kai wani mummunan hari a yankin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.
A bara Amurka ta yi tayin ladan kudi dala miliyan 5 ga wanda ya ba da bayanai game da shi.
Rundunar sojin Isra'ila ta ki cewa komai kan rahoton, amma irin wannan harin ya yi dai dai da kudurin da birnin na Kudus ya yi na kashe wasu manyan shugabannin Hamas, a yayin da yakin da Hamas a Gaza ya kusa cika watanni uku.
Arouri ya jagoranci kasancewar Hamas a yankin yammacin gabar kogin Urdun da Isra'ila ta mamaye. Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi barazanar kashe shi tun ma kafin kungiyar mayakan ta kai mamaya a kudancin Isra'ila a harin na watan Oktoba.
Dandalin Mu Tattauna