WASHINGTON, D. C. - Karim Berthé, wani babban jami'i a Hukumar kula da mu’adinan karkashin kasa da aikin hakar mu’adinai National Geology and Mining Directorate, ya tabbatar da cikakkun bayanai ga Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press kuma ya kira lamarin hadari.
Akwai kusan mutane 100 a cikin mahakar ma'adinan a lokacin rugujewar, a cewar Abdoulaye Pona, shugaban hukumar kula da ma'adinan kasar Mali, wanda ya je wurin.
Ana gudanar da bincike kan musabbabin rugujewar da ta faru a gundumar Kangaba da ke kudu maso yammacin yankin Koulikoro a ranar Juma'a. An fara ba da rahoto a ranar Talata a cikin wata sanarwa da ma'aikatar ma'adinai ta fitar da ta kiyasta cewa "da yawa" masu hakar ma'adinai sun mutu.
Irin wadannan bala'o'i sun zama ruwan dare a kasar Mali, wadda ita ce kasa ta uku da ke samar da zinari a Afirka. Masu aikin hakar kananan ma'adinai na yau da kullun ana zarginsu …. Say instead, Ana zargin masu aikin hakar kananan ma'adinai na yau da kullun da yin watsi da matakan tsaro, musamman a wurare masu nisa.
Bethe yace, "Dole ne jihar ta samar da tsari ga wannan fannin na hakar ma'adinai don guje wa irin wadannan hadurruka a nan gaba," in ji Berthé.
Sanarwar ma'aikatar ma'adinai ta "yi matukar nadamar" rugujewar, kuma ta bukaci masu hakar ma'adinai da al'ummomin da ke zaune kusa da wuraren hakar ma'adinai su "kiyaye ka'idojin kariya."
Dandalin Mu Tattauna