Kotun kasa ta rubutawa kotun tsarin mulki wasika a farkon watan Yuni domin fayyace matsayin dan majalisa Hama Amadou bisa la'akkari da hukuncin da aka yanke masa a watan Maris na 2017, sakamakon samunsa da hannu a wata badakalar siyan jarirai. Bayan nazarin wannan wasikar, alkalan kotun tsarin mulkin sun bukaci majalisar dokokin kasa da ta maye gurbin Hama Amadou da mataimakinsa Garba Hema.
Me kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar game da wannan hukuncin?
Dakta Boubakar Amadou Hassan, shugaban kungiyar masanan dokokin tsarin mulki a Nijar ya ce, aya ta 8 na babi 147-148 ne ya bai wa kotun hujjar yanke wannan hukunci.Inda tun a ranar 19 ga watan Yunin 2018, kotun ta cire Mallam Hama Amadou daga mukaminsa na dan majalisar dokoki.
Haka zalika, baya ga rasa mukaminsa na dan majalisa, jagoran 'yan adawa Hama Amadou na fuskantar barazanar rasa 'yancinsa na tsayawa takara a 2021 kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.
A cewar masanin, duk wanda aka yankewa hukuncin zaman gidan kaso na shekara guda kamar yadda aka yi wa Hama Amadou, kuma ba a wankeshi ba, zai yi wuya ya tsaya a matsayin dan takara. Domin ita wannan kotun ke da damar tantance wadanda suka cancanci tsayawa takara a kasar saboda haka da kyar ta amince da shi a zaben shekarar 2021.
"Kenan a siyance, makomarsa ta shiga matsala," inji Dakta Boubakar
A farkon watan Yunin 2018, Jamhuriyar Nijar da Faransa suka rattaba hannu akan wasu yarjejeniyoyin da suka shafi harkokin shari'a ciki har da matakin da 'yan adawa ke ganin na kokarin taso keyar Hama Amadou ne daga Faransa inda ya kwashe shekaru yana hijira domin a gurfanar da shi a gaban shari'a. Kawo yanzu, hukumomin Nijar ba su nuna wannan bukatar ba a fili.
Saurari rohoton Sule Mumini Barma
Facebook Forum