Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince zata kafa gandun dajin kiwon shanu a wasu jihohi goma.
An cimma matsayin samar da gandun dajin ne a wani taron sake fasalin kiwo a Najeriya da majalisar tattalin arzikin kasar ta gudanar a Abuja.
Jihohin da zasu amfana da shirin a karo na farko sun hada da Adamawa, Binuwai, Ebonyi, Edo, Kaduna, Nasarawa, Oyo, Plateau, Taraba da Zamfara.
Yayinda yake gabatar da shirin sakataren wani sashen kwamitin majalisar tattalin arzikin kasar Dr. Andrew Kwaskwari y ace shirin da ake kyautata zaton zai kawo karshen yawan tashin hankali dake aukuwa tsakanin manoma da makiyaya, gwamnati zata kashe Naira biliyan 70 cikin shekara uku a jihohi goman da za’a fara.
Gwamnan jihar Plateau Barrister Simon Lalong shugaban kwamitin a yankin arewa ta tsakiya y ace gwamnatin tarayya ta amince da shirin kuma shugaban kasa yace kowace jiha ta ware wuri, kuma gwamnati zata gina makarantu da asibitoci saboda shugaban baya son ya sake jin tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma.
Gwamnan jihar Nasarawa daya daga cikin jihohin da gwamnatin tarayya zata kafa gandun dajin, yace zasu tabbatar da kiyaye doka ta yadda manomi ba zai cuci makiyayi ba haka ma makiyayi ba zai cuci manomi ba.
Jihar Binuwai ma na kan gaba wajen kebe wuraren kiwo saboda tuni ta haramta yin kiwo a fili. A taron masu ruwa da tsaki a jihar gwamnan jihar Samuel Ortom ya jaddada goyon bayansa ga samar da wuraren kiwo ma makiyaya, tare da cewa hanya mafi a’ala it ace kebe gandun daji domin kiwo.
A jihar Plateau kuma sarkin Wase Alhaji Muhammad Sanda Haruna ya tabbatar da samar da gandun gaji na kiwo a kananan hukumomin Wase da Kanam.
A saurari rahoton Zainab Babaji domin karin bayani
Facebook Forum