Yayinda Shugaba Muhammad Buhari ke rabtaba hannu akan kasafin kudin shekarar 2018, wanda ya samu jinkirin wata shida, ya ce bai ji dadin sauye-sauyen da ‘yan majalisa suka yiwa kasafin kudin ba.
Majalisa ta cire wasu muhimman ayyuka da suka danganci bunkasar tattalin arzikin kasa. Haka kuma majalisar ta zabge kudade har Naira biliyan 347 da suka shafi ayyuka 4700 sannan ta kara Naira biliyan 578 akan wasu ayyuka 6403.
Ayyukan da majalisar ta cire suna da mahimmanci amma kuma sabbin da aka cusa cikin kasafin zasu yi wuyar aiwatarwa kamar yadda shugaban ya fada.
Sai dai mataimakin masu rinjaye a majalisar dattawa Bala Ibn Na’Allah ya bada hujjar da ta sa suka yi sauye-sauyen. Yace tsarin mulki ya tanadi a kai kasafin kudin majalisa domin a tabbatar ba’a cuci kowa ba. A saboda haka majalisa tayi kwaskwarima ne domin kada a cuci wani bangare.
‘Yan majalisar sun kara farashin danyen man fetur daga dala 45 zuwa dala 51.
Sanata Danjuma Goje shugaban kwamitin kula da kasafin kudi ya bayyana cewa basu ne suka kara kudin man da kansu ba. Sun yi shawara da shugaban kasa da sauran mukarrabansa domin a samu karin kudi. Karin an yi anfani dashi ne wajen magance wasu abubuwa da suke damu mutane. Misali, an kara wa ma’aikatar hanyoyi fiye da Naira biliyan 109. An baiwa sabbin jami’o’i da aka bude guda 12 kudi na musamman.
A bangaren kiwon lafiya Sanata Goje y ace shekaru hudu da suka gabata aka kafa dokar cewa kashi daya na kasafin kudi a ba harkokin kiwon lafiya. Ba’a taba yin hakan ba amma a wannan shekarar sun yi. Sun ware makudan kudi Naira biliyan 57 domin kiwon lafiya.
A saurari rahoton Medina Dauda da karin bayani
Facebook Forum