Cutar kwalera ta barke a jihar Neja. Kawo yanzu mutane 120 ne suka kamu kuma tuni 10 suka mutu.
Mutanen da suka mutu sun fito ne daga kananan hukumomi guda hudu, da suka hada da Bako, Lavun, Kacha da Bida.
Kwamishanan kiwon lafiya na jihar Dr Mustapha Jibrin ya tabbatar da mutuwar mutane bakwai a Bida. Kazalika kwamishanan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta bada Naira miliyan 25 domin shawo kan yaduwar cutar da kuma taimakawa wadanda suka kamu da cutar da magunguna.
Baicin taimakon kudin da gwamnatin jihar ta yi ana kuma wayar wa jama’a kai ta kafofin labarai kamar rediyo tare da yin tarurruka domin baiyana matakan da suka kamata jama’a su dauka na kariya
Hukumar kula da yara kanana ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta kai dauki jihar. Malam Muhammad Khalil babban jami’in hukumar dake kula da jihar Neja ya ce aikinsu ne su taimakawa gwamnati domin ta aiwatar da ayyukanta yadda suka kamata musamman ga yara.
A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Facebook Forum