Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Bada Belin Tsohon Minista Agunloye Akan Naira Milyan 50


A yau, Alhamis, 11 ga watan Janairu, Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie na babbar kotun babban birnin tarayyar Najeriya dake zamanta a unguwar Apo, ya bada belin tsohon Ministan Lantarki da Karafa na kasar, Olu Agunloye, akan kudi naira milyan 50.

An gurfanar da Agunloye a gaban kuliya ne akan wasu tuhume-tuhume bakwai (7) dake da nasaba da badakalar bada kwangila da cin hanci da rashawa a ranar laraba.

Alkalin ya bada umarnin tsare tsohon ministan a gidan Gyaran Hali na Kuje ne gabanin kammala saurare da zartar da hukunci akan bukatar bada belinsa.

Da yake gabatar da bukatar bada belin, lauyan tsohon ministan, Adeola Adedipe, ya bukaci kotun ta bada belin wanda yake karewa kodai bisa la’akari da kimarsa ko kuma ta hanyar yin sassauci.

A cewarsa babu fargabar tserewa game Agunloye kuma akwai rashin kyakkyawar fahimta daga bangaren masu kara game da lamarin.

Haka kuma, Adedipe ya bukaci kotun da kada ta gindaya masu rike da mukaman gwamnati a matsayin wadanda zasu tsayawa wanda yake karewa.

Babban lauyan ya kuma yi tsokaci akan cewar sashe na 352 na kundin hukunta manyan laifuffukan Najeriya yayi maganin fargabar kulla makarkashiyar da bangaren masu kara ya ayyana.

Adeola ya ci gaba da cewar a karkashin wannan sashe, za’a cigaba da shari’a tare da yanke hukunci yadda ya dace, matukar aka bada beli koda kuwa wanda ake karar ya tsere.

Saidai, lauyan masu kara ya kalubalanci bukatar bada belin.

Da yake zartar da hukunci akan bukatar bada belin, Mai Shari’a Onwuegbuzie yace ra’ayin kotun ya karkata ga amincewa da bukatar bada belin wanda ake kara.

Don haka ya bada belin wanda ake kara akan kudi naira milyan 50 tare da umartarsa ya gabatar da mutane biyu da zasu tsaya masa akan naira milyan hamsin-hamsin kowannensu.

Wajibi wadanda zasu tsaya masan su zama fitattun mutane masu abun hannu dake zaune a birnin Abuja.

Haka kuma, dole ne mutanen su mallaki gidaje ko filayen da darajarsu ta kai naira milyan 300 da cikakkun takardu.

Har ila yau, wajibi mitanen su mika kwafen katunan shaidarsu dana fasfo din tafiye-tafiyensu ga kotun.

Kuma wajibi ne wanda ake karar ya mika fasfo din tafiye-tafiyensa ga kotun tare da hallara duk sa’ilin da za’a saurari shari’arsa.

An dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Febrairu mai zuwa.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati na gudanar da bincike akan Agunloye game da kwangilar aikin lantarkin Mambila ta fiye da dala biliyan shida.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG