Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Azerbaijan Na Makokin Mutane 38 Da Suka Mutu A Hadarin Jirgin Sama


Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev ya ayyana yau Alhamis ta zamo ranar makoki tare da soke shirin tafiyarsa zuwa Rasha domin halartar taron kolin kasashen da suka balle daga tsohuwar tarayyar Soviet (CIS).

A yau Alhamis kasar Azerbaijan ke fara makoki bayan da wani jirgin saman fasinja daga ayarin jiragen gwamnatin kasar ya rikito a yammacin Kazakhstan a ranar Kirsimeti, inda ya hallaka 38 daga cikin mutane 67 din dake cikinsa.

Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev ya ayyana yau Alhamis ta zamo ranar makoki tare da soke shirin tafiyarsa zuwa Rasha domin halartar taron kolin kasashen da suka balle daga tsohuwar tarayyar Soviet (CIS).

Mataimakin Firai Ministan Kazakhstan Kanat Bozumbayev ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Rasha (Interfax) cewa hatsarin ya hallaka mutane 38, yayin da ma'aikatar agajin gaggawa ta kasar ta bada rahoton cewa mutane 29 sun tsallake rijiya da baya, "ciki har da yara 3, da ke samun kulawa a asibiti".

Kamata yayi jirgin samfurin Embraer 190 da ya tashi daga Baku babban birnin Azerbaijan zuwa Grozny da ke yankin Chechnya a kudancin Rasha ya kada zuwa arewa maso yamma, amma sai ya baude da nisa zuwa ketaren tekun Caspian. Ya fadi a jiya Laraba kusa da birnin Aktau na Kazakhstan.

Kamfanin jiragen saman Azerbaijan ya bada rahoton cewa fasinjoji 62 ne da ma'aikata 5 ke cikin jirgin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG