Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Son Gwamnatin Da Za Ta Yi Wa Jama’a Aiki Ba Kawai Ta Mulke Su Ba – Mazaunin Abuja


Masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Abuja
Masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Abuja

Dubban jama'a na ci gaba da yin zanga zanga a kan tituna a Najeriya, a Abuja babban birnin tarayyar kasar masu zanga-zangar sun yi ta rera wakoki yayin da suke guje wa barkonon tsohuwa da 'yan sanda suka harba.

A ranar Alhamis ne dai ‘yan Najeriya suka fara fitowa kan tituna suna neman a sauya wasu manufofin gwamnatin kasar, ciki har da cire tallafin man fetur da aka yi a shekarar da ta gabata.

Zanga zangar ta gama da za a yi tsawon kwanaki goma, an yi ta a biranen Najeriya da yawa, duk da arangamar da aka yi da jami'an tsaro a wasu wurare.

Daya daga cikin masu zanga zangar, Wisdom Chimuanya, mazaunin birnin Abuja ne, ya ce “Mun cancanci mu ci moriyar albarkatun da muke da su, muna da albarkatun ma’adinai, muna da albarkatun kasa, an albarkaci jama’a da abubuwa da yawa. Muna son gwamnatin da za ta yi wa jama’a aiki ba kawai ta mulke su ba, ya kamata shugaban kasa ya biya bukatun jama’a, abin ya isa haka."

A lokacin bikin rantsar da shi a watan Mayu, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da kawo karshen biyan tallafin man fetur. Ba a dade da hakan ba, shugaban ya kuma dauki matakin barin naira ta nema wa kanta daraja. Bayan haka, hukumomin kasar suka kuma kara kudin wutar lantarki da fiye da kashi 200.

NEPA
NEPA

Masu zanga-zangar sun ce wadannan manufofin sun sanya rayuwar yau da kullum zama da wahala.

Da ta ke maida martani, rundunar ‘yan sandan kasar ta ce ta yi amfani da barkonon tsohuwa ne don wargaza masu zanga-zangar.

Benneth Igweh, shi ne kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya, ya ce kotu ta ba da umurnin ne domin hana duk abin da zai kawo cikas ga al’amuran yau da kullum a kewayen birnin.

"Ba umarnina ba ne, ba umarnin sufeto janar na 'yan sanda ba ne, ba umarnin kowa ba ne, umarnin kotu ne," a cewar Igweh.

Kafofin yada labaran kasar dai sun ce an kashe mutane sha uku a fadin kasar a yayin zanga-zangar.

Hukumomi a jihohin Borno da kuma Kano sun sanya dokar hana fita a ranar Juma’a domin shawo kan tarzomar da aka yi a lokacin zanga zangar.

Masu Zanga-zanga
Masu Zanga-zanga

A watan da ya gabata, 'yan majalisar dokokin Najeriya sun yi alkawarin ba da rabin albashinsu har tsawon wata shida ga 'yan kasar, sannan hukumomi sun sassauta haraji kan wasu kayayyakin abinci da suka hada da alkama don rage farashinsu.

A ranar Litinin, Najeriya ta rattaba hannu a kan sabon mafi karancin albashi. Sai dai masu zanga-zangar sun ce wadannan matakan ba su wadatar ba, sun kuma sha alwashin mamaye tituna har sai an dawo da tallafin man fetur.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG