Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Zai Yiwa Kasa Jawabi


Bola Tinubu
Bola Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar kasa kai tsaye a gobe Lahadi 4 ga watan Agusta, 2024, da misalin karfe 7 na safe agogon kasar.

A sanarwar da mai magana da yawun shugaba Tinubun, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce “Kafafan yada labarai na talabijin, rediyo da sauran na intanet za su iya tarar shirin kai tsaye daga gidan talabijin na kasa NTA da gidan rediyon na tarayya FRCN domin yaba jawabin shugaban kasa.

Sanarwar ta kara da cewa za’a sake maimaita watsa shirin a gidan talabijin na NTA da na rediyo FRCN da misalim karfe 3 na yamma da kuma karfe 7 na dare agogon kasar.

Wannan na zuwa bayan da matasa su ka fara wata zanga-zangar gama gari a fadin kasar a ranar Alhamis 1 ga watan Agusta kan tsadar rayuwa da sauran matsaloli da su ke addabar kasar.

Matasan dai suna kokawa kan tsadar man fetur, wutar lantarki, kayan masarufi da dai sauran su, inda suke ta kiraye-kiraye da gwamnatin ta dauki matakai na kawo mafita daga wannan mawuyacin hali da al’ummar kasar take fuskanta na fatara da talauci.

Gwamantin tarayyar kasar ta nemi matasan da su kara ba ta lokaci domin tuni ta fara daukan matakai don magance wadannan matsaloli.

Sai dai matasan sun ce manufofin gwamnatin shugaba Bola Tinubu ne da ta dauka suka kara jefa kasar cikin wannan hali na matsi.

A rana ta biyu ta zanga-zagar a wasu wurare an samu arangama da jami’ai da wasu masu zanga-zagnar, inda har aka yi asarar rayuka da dukiya.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kame masu zanga-zanga da dama tare da harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu yunkurin yin tattaki zuwa ofisoshion gwamnati a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, a rana ta uku ta zanga-zangar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG