Jaridar Izvestiya da ake wallafa a kullum, ta ruwaito cewa, kasafin kudin da aka warewa tashar daga wannan shekare zuwa shekara ta 2025 ya kai dala biliyan 3.3 ko kuma kusan dala miliyan 330 a kowace shekara.
Hakan na nufin an samu ragin kashi goma cikin 100 daga daftarin da aka tsara tun a watan Aprilun bara.
Hukumar da ke kula da ayyukan zuwa sama jannati na Rasha na daga cikin wuraren ayyuka guda biyar da take da su, wadanda ta ke aiki tare da ma’aikata daban-daban domin gudanar da bincike.
Rasha na taka muhimmiyar rawa wajen safarar kwararrunta daga doron kasa zuwa sararin samaniya, tun bayan da Amurka ta janye kayayyakin aikinta da kwararrunta daga tashar.
Amurka dai ita tafi kowace kasa kashe kudaden raya wannan tasha tun bayan da ta kaddamar da ayyukanta a shekarar 1998, inda take kashe dala biliyan uku a duk shekara.