Mr. Nicholson Kay jakadan Majalisar Dinkin Dniya a Somaliya yace kasar na farfadowa a hankali.
Mr. Kay ya furta kalamun ne yayinda yake gabatar da rahotonsa ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Rahoton tamkar ba majalisar ne masaniya akan abubuwan da ya yi cikin shekaru biyun da ya yi yana zaman jakadan majalisar a Somalia.
Inji Mr. Kay kasar Somalia ta soma fita daga rudanin da suka dabaibayeta na 'yan shekaru da dama.
Yanzu kasar tana fuskantar matsaloli ne irin na kasashen dake farfadowa maimakon wadda take wargajewa.
Ana shirin shirya zabe badi wanda ko shakka babu zai zama zakaran gwajin dafi. Shi ne kuma zai nuna ko kasar zata cigaba da farfadowa ko kuma ta wargaje. Mr. Kay yace dole ne a yi zaben kuma akan lokaci a kuma tabbatar kowane bangaren kasar ya samu wakilci.
Ya yi gargadin a tabbatar an yi zabe mai inganci, wanda ya fi na shekarar 2012 inganci sosai.