Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Kuryar Afirka Zasu Samu Dala Miliyan Dubu Takwas


Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon

Tarayyar Turai, Bankin Duniya, Bankin Islama da Bankin Cigaban Afirka Sun samar ma kasashen kuryar Afirka tallafin kudi mai tsoka a karkashin shirin Majalisar Dinkin Duniya.

Kasashe da suke kuryar Afirka zasu amfana da kuddi sama da dala miliyan dubu takwas saboda su gudanar da ayyukan ci gaba, karkashin wani sabon shiri da aka bayyana jiya a Habasha.

Manyan hukumomin duniya ne suka yi alkawarin,wadanda suka hada da kungiyar tarayyar turai, da kuma bankunan ayyukan raya kasa da kasa su uku. An bada sanarwar yayinda babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon, ya jagoranci wani taro da shugabannin kasashe da suke yankin da wadanda suka kware a fannin kudi.

Za’a a yi amfani da kudaden ne a kasashe takwas da suka hada Djibouti, Ertrea, Ethiopia, da Kenya, da Somalia, da Sudan da Sudan ta Kudu, da kuma Uganda. Kuma an bada kudaden ne da nufin rage talauci da kuma samar da hanyoyin bunkasa tattalin arziki a fadin yankin baki daya.

Kungiyar tarayyar turai itace ta bada kaso mafi tsoka na dala milyan dubu uku da miliyan dari bakwai. Bankin duniya da Bankin raya Afirka suka bada dala miliyan dubu daya da miliyan dari takwas ko wane daga cikinsu, yayinda Bankin Islama mai ayyukan raya kasa yayi alkawarin zai bada dala miliyan dubu daya da zai auna kan kasashen Djibouti, da Somalia, da Sudan da Uganda.

Kasashen da suke kuryar Afirka suna da dumbin albarkatun da suke karkashin kasa, amma galibin su suna fama da tashe tashen hankula da suka hana zaman lafiya, wanda ya janyo koma bayan tattalin arziki.

Shugaban babban bankin duniya Jim Yong Kim, yace kudaden zasu kasance babbar dama ga jama’ar kasashen da suke kuryar Afirka wajen samun ruwan sha mai tsabta, da abinci mai gina jiki, da kiwon lafiya, da il Imi da kuma ayyukan yi.

XS
SM
MD
LG