Mayakan kungiyar al-Shabab sun kai hari kan wani otel dake Mogadishu babban Birnin kasar ta Somalia. Sun kashe akalla mutane tara da suka hada da wani jakadan kasar.
Shaidun gani da ido sun ce hare-haren na jiya Juma’a akan otel mai suna Maka al-Mukarama sun fara ne da tayar da bom kafin ‘yan bindiga guda biyar su kutsa cikin otel din.
Gurey Haji Hassan wanda ya kasance daya daga cikin masu otel din kuma manajan wurin yace ‘yan bindigan sun yi da kofar baya inda suka tayar da bom kafin su kwace ikon otel din. Wasu dakarun gwamnatin kasar ta Somalia na musamman da ake kira Gashaan sun shiga otel din domin farautar ‘yan bindigan.
Wani jami’in asibitin Birnin Mogadishu da aka sani da suna Medina ya shaidawa Muryar Amurka Sashen Somalia cewa jakadan Somalia na kasar Switzerland Yusuf Mohammed Ismail Bari Bari an kawo shi asibitin da mugun rauni amma daga bisani sai rai yayi halinsa