Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar al-Shabab Ta Kashe Dalibai 147 a Kenya


'Yan sanda a garin Garissa, Afrilu 2, 2015.
'Yan sanda a garin Garissa, Afrilu 2, 2015.

Mayakan kungiyar al-Shabab mai tsatsauran ra'ayin addinin Islama ta mamaye wata jami'a a Kenya inda ta kashe dalibai 147

Jami’an kasar Kenya sun ce an kawo karshen mamayar kwana daya da aka yiwa wata jami’a a gabashin Nairobi babban birnin kasar, da ya yi sanadin mutuwar mutane dari da arba’in da bakwai, da kuma ‘yan ta’addan al-shabab hudu.

‘Yan sanda da wadanda suka tsallake rijiya da baya sun ce, ‘yan bindiga sun kutsa cikin jami’ar Garissa ranar Alhamis, suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi.

Sai dai wadansu daliban sun ce maharan sun rike ware dalibai kirista daga Musulmi suna garkuwa dasu.

Jami’an tsaro sun yiwa makarantar kawanya, suka fafata da mayakan na tsawon sa’oi goma sha biyar, suka ceto dalibai dari biyar, wadanda harin ya rutsa dasu.

Ministan cikin gida Joseph Nkaissery yace, ‘yan bindigan hudu sun yi damara da nakiyoyi suka tarwatse kamar bomb lokacin da ‘yan sanda suka harbe su.

Kungiyar al-shaban tace harin ramuwar gayya ce sabili da matakin sojin da rundunar sojin kasar Kenya ta dauka a Somalia,tushen mayakan kishin Islaman al-Shabab.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG