Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kenya Sun Ja Daga a Garin Garissa Bayan Harin Ta'adanci


Wasu da suka yi asarar 'yanuwa a Garissa
Wasu da suka yi asarar 'yanuwa a Garissa

Yayinda ake tantance daliban da suka tsira da rayukansu a harin da kungiyar al-Shabab ta kai jami'ar Garissa sojojin Kenya sun yiwa garin kawanya

Bayan harin biyu ga watan Afirilu sojojin kasar Kenya sun ja daga a garin Garissa domin dakile duk wani sabon harin ta'adanci.

Karamar hukumar Garissa da kuma wadansu kananan hukumomi uku da kungiyar al-Shabab take yawan yiwa barazana suna karkashin dokar hana fita ba dare ba rana.

Garin Garissa ya fuskanci yawan hare-haren bamabamai da gurneti cikin 'yan shekarun nan wadanda ake dora alhakin akan mayakan al-Shabab na kasar Somalia to amma babu wanda ya kai na makon jiya muni.

Daliban da suka tsallake rijiya da baya da yanzu suna jinya a asibiti sun bada bayanin irin mummunan abun da ya faru a ranar. Wata daliba mai suna Quintin Ayango tace ta tashi da safe domin ta yi karatu lokacin da aka fara kai harin. Da ta fita waje sai ta ga wasu mutane uku da bata saba gani ba dauke dauke da bindigogi. Sai ta nemi wuri ta buye.

Quintin tace ta wuni ta na jin karar biindiga daga inda ta boye lokacin da aka kashe abokanta dalibai a wani aji dake kusa. Quintin tace ta yi adabo da garin Garissa.

Kungiyar al-Shabab tace harin ramuwar gayya ce saboda yadda wai ake tozartawa Musulmai a Kenya da kuma rawar da kasar Kenya ke takawa a Somalia. To amma Musulmin dake kasar Kenya din sun kushewa kungiyar. Wadansu shugaban musulmai har ma kira suka yi a tasa keyar 'yan Somalia dake gudun hijira zuwa kasarsu.

A cikin jawabin shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ranar Asabar yace 'yan ta'ada suna kulla makarkashiyar kai hare-haren ne a cikin kasar Kenya kana ya yi alkawarin daukan kwararan matakai kan wadanda suke da hannu. Yace zasu dauki matakan da doka ta tanada fiye da yadda ake yi da can.

Yanzu dai ana cigaba da tantance dalibai fiye da dari takwas domin a san adadin wadanda suka rasa rayukansu ko kuma suka jikata.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Shugaba Kenyatta yace ba zasu kyale 'yan ta'ada su cigaba da rayuwarsu yadda suka saba ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG