Wani tsohon kwamandan kungiyar Al-Shabab dake kasar Somalia ya fito fili yace shi ya daina ta’adanci kuma yayi allawadai da rikicin da abokansa ke haddasawa.
Zakariya Ismail Hersi wanda ya taba zama babban jami’in liken asiri na kungiyar dake da alaka da al-Qaida ya mika kansa ne ga jami’an Somali watan Disamban bara.
Yace “Daga yau zan dinga bayyana ra’ayoyina da akidojina ta hanyar lumana da fahimta” inji shi. Hersi yayi furucin ne a wani taron manema labarai da ya wakana a Birnin Mogadishu jiya Talata.
Da ya mayarda hankali akan ‘yan kungiyar al-Shabab din Hersi yace “Ina gargadinku abokanaina ku nemi warware matsalolinku ta hanyar lumana da tattaunawa cikin kwanciyar hankali.
Idan ba’a manta ba a watan Yunin shekarar 2012 Amurka ta bada tayin tukuicin dala miliyan uku ga duk wanda ya bayar da labarin da zai kaiga kama Hersi.
Da ma an zargi Hersi din da kasancewa na hannun daman Ahmed Abdi Godane tsohon shugaban kungiyar al-Shabab.