Kasashen Mali, Burkina Faso da Nijer da ke karkashin mulkin soja sun ba da sanarwar ficewa daga sahun kasashe mambobin ECOWAS sakamakon abin da suka kira rashin gamsuwa da yadda kungiyar ta kauce wa ainahin turbar da aka kafa ta,.
Kasashen har ila yau suna zargin kungiyar da kasancewa barazana ga zaman lafiya a yankunansu.
Kakakin majalisar CNSP, Kanal Abdourahamane Amadou, ya bayar da sanarwar hadin gwiwar kasashen uku a kafar talbijan RTN Mallakar gwamnatin ta Nijear da misalin karfe 2 na ranar Lahadi 28 ga watan Janairun 2024 kwana daya kenan bayan ziyarar da wasu ministocin Burkina Faso da na Mali suka gudanar a birnin Yamai.
Sanarwar wace ta zo a wani lokaci da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ke yunkurin shiga tsakanin a rikicin siyasar da ya samo asali daga juyin mulkin da sojojin CNSP suka yi wa shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
Wasu na ganin wannan mataki da kasashen suka dauka na iya zama mafarin bude wani sabon babi a dambarwar da ke ci gaba da daukan hankulan kasashen duniya.
Dandalin Mu Tattauna