Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ba A Fara Sayar Mana Da Danyen Man-Fetur A Naira Ba. Kungiyar CORAN


Wata rijiyar hakar mai karkashin teku.
Wata rijiyar hakar mai karkashin teku.

Gamayyar Kamfanonin Tace Albarkatun Mai a Najeriya (CORAN), sun bayyana cewa har yanzu babu wani memban kungiyar da aka fara sayarwa danyen mai da kudin Naira. Sakataren hulda da jama’a na kungiyar Echie Idoko, ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai.

Echie Idoko, ya ce “idan za a iya tunawa, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya bada umarnin a fara sayar musu da danyen mai da kudin Naira, a lokacin wani taron Majalisar zartaswa da ya gudana a fadar shugaban kasar, wanda hakan zai taimaka musu wajen samun isasshen man da zasu tace a kamfanonin su cikin sauki”.

Idoko, ya kara da cewa “duk da wannan sanarwa ta Shugaban ƙasa, ba su fara cin gajiyar hakan ba, ko da yake akwai bukatar wasu matakai da ka’idodi da ya kamata su bi, kafin a fara sayar musu da danyen man a Naira”.

Wakiliyar Sashen Hausa ta yi kokarin jin ta bakin hukumar kula da albarkatun mai ta ƙasa (NMDPRA) bisa jinkirin fara sayar da danyen man a farashin Naira da kungiyar CORAN ta koka akai, har izuwa hada wannan rahoto, hakata bata cimma ruwa ba.

Sai dai ta tuntubi babban mai bincike na kungiyar dillalan man-fetur ta IPMAN, Yakubu Ali Bulkadimka game da tsaikon da matatun mai ke fuskanta wajen fara sayan danyen man a Naira, ya ce “ wadannan jinkiri da sauran tsaiko da harkar Man-Fetur ke fuskanta a kasar, alhaki ne da yake kan hukumar kula da albarkatun mai ta NMDPRA, da kuma rashin tsari na aiwatar da abu cikin lokaci, ya kuma zargi hukumar da rike musu kudaden da suke binta bashi.

Mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Nasir Marmara, ya ce jinkirin aiwatar da irin wannan muhimman ayyuka da zai amfani talakan Najeriya ba sabon abu ba ne a kasar, ganin cewa cin hanci da rashawa na tasiri a wasu ma’aikatun kasar.

Masana tattalin arziki irinsu Dakta Isa Abdullahi Kashere, na ganin tafiyar kunkuru wajen aiwatar da ayyukan da suka dace a kasar, yana yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, da kuma karawa talaka kuncin rayuwa.

Ƴan Najeriya dai na cigaba da koka wa bisa karancin Man-Fetur a kasar da kuma tsadarsa.

Ga dai Rukaiya Basha daga Abuja Najeriya dauke da rahoto cikin sauti:

Har Yanzu Ba A Fara Sayar Mana Da Ɗanyen Man-Fetur A Naira Ba. Kungiyar CORAN.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG