Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatar Kudi, NNPCL Sun Fara Shirin Sayar Da Danyen Mai A Naira

Shugaban NNPCL, Mele Kyari, dama, Mr. Wale Edu, tsakiya (Facebook/NTA)
Shugaban NNPCL, Mele Kyari, dama, Mr. Wale Edu, tsakiya (Facebook/NTA)

Kwararru a fannin tattalin arziki sun ce daukan wannan mataki zai taimaka matuka wajen rage hauhawar farashin mai.

A wani mataki na kokarin aiwatar da umarnin da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar na a fara sayarwa da matatun man cikin gida man fetur a naira, ma’aikatar kudi da kamfanin man kasa na NNPCL sun fara zama a ranar Laraba a Abuja.

A karshen watan Yuli Tinubu ya ba da umarni ga kamfanin na NNPCL da ya fara sayarwa da ‘yan kasuwar cikin gida mai a naira, a wani mataki na sauke farashin man.

Ministan kudi da tattalin arziki Mr. Wale Edun ya gana da masu ruwa da tsaki a ofishinsa da ke Abuja a wani yunkurin na ganin an aiwatar da wannan umarni.

Daga cikin mahalarta taron har da shugaban kamfanin man na NNPCL, Mele Kyari da Ministan albarkatun mai, Mr Heineken Lokpobiri.

Kwararru a fannin tattalin arziki sun ce daukan wannan mataki zai taimaka matuka wajen rage hauhawar farashin mai.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG