Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Shell Zai Sayar Da Sashen Kasuwancin Mai Na Najeriya


Kamfanin Man Shell
Kamfanin Man Shell

Kamfanin Shell ya fada a ranar Talata cewa ya cimma matsayar sayar da kasuwancinsa na teku a yankin Niger Delta na Najeriya ga wata hadakar kamfanoni, a wata yarjejeniya da ta kai dala biliyan 2.4.

WASHINGTON, D. C. - Mataki na baya-bayan nan da kamfanin makamashin ya dauka na takaita yawan hada-hadarsa a kasar ta yankin Afirka ta Yamma sakamakon korafe-korafen da aka dade ana yi na gurbata muhalli da masana’antar ta man fetur ke haddasawa.

Shell ya bayyana hakan a matsayin hanyar daidaita harkokin kasuwancinsa a kasar da ya kwashe shekaru da dama yana fuskantar koma baya game da malalar mai da ta lalata koguna da gonaki da kuma ta'azzara rikici a yankin da ya fuskanci tashin hankalin 'yan bindiga na tsawon shekaru.

Zoe Yujnovich, daraktan hadakar hakar mai da iskar gas na kamfanin Shell ya fada a cikin wata sanarwa cewa "wannan yarjejeniya ta kasance wani muhimmin ci gaba ga Shell a Najeriya, wanda ya yi daidai da aniyar mu a baya na ficewa daga hako mai a yankin Neja Delta." Wannan zai taimaka wajen "sauƙaƙe kasuwancin mu da kuma mai da hankali kan saka hannun jari mai inganci nan gaba a Najeriya dangane da aikin hako danyen mai ta ruwa da iskar gas."

Hadakar kamfanonin da zai saya shine Renaissance, wanda ya kunshi ND Western, Aradel Energy, First E&P, Waltersmith da Petrolin, in ji Shell. Bayan fara biyan dala biliyan 1.3, babban kamfanin samar da makamashi da ke Landan ya ce zai sami karin dala biliyan 1.1.

Kadarorin da Shell zai sayar mallakar kamfanin mai na gwamnatin Najeriya na NNPC ne, wanda ke da kaso 55% na hannun jari. Don kammala yarjejeniyar, dole sai gwamnatin Najeriya ta amince. Shell ne ya ke sarrafa kadarorin kuma yana da hannun jari na kashi 30%, tare da ragowar hannun jari na Total Energies na Faransa na kashi 10% da Eni na Italiya mai kashi 5%.

Kaddarorin sun hada da layukan hako ma'adinan teku guda 15 da kuma wasu tashoshin bakin ruwa uku, in ji kamfanin.

Amma kafin a kammala sa hannu a yarjejeniyar sayarwar masu fafutuka na son a fara tsaftace gurbatattun muhallan.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG