A karar da monoman suka shigar a kotun sun nemi cewar kamfanin hako danyen mai na Shell ya biya su diyyar miliyoyin dalolin Amurika don bata masu muhalli da gurbata ruwan yankin,
Yanzu kotu ta bada hukuncin cewa kamfanin Shell ya biya diyya ga manoman da abin ya shafa. Haka kuma kotun ta bukaci kamfanin na Shell da ya dauki matakan kare kara faruwar haka nan gaba.
Bayan wannan hukuncin na kotun, jama'ar yankin Neja Dalta sun bayyana ra’ayoyinsu wa wakilin Muryar Amurka.
Wani a cikin su ya ce, "muna matukar godiya ga Allah game da wannan hukunci bayan shekaru 13 muna kai da kawowa akan wannan lamari da ya shafi muhallinmu da kuma gurbata mana ruwa. Ya kara da cewa wannan ranar farinciki ce don an mana adalci."
Ya ce dole ne idan suna aiki inda akwai mutane su rika kula da rayuwar jama’a, da kuma muhalli da ka’idojin kasa.
A saurari rahoto cikin sauti daga Abubakar Lamido Sakkwato: