Lamarin ya faru ne a garin al’umomin Kom Kom dake karamar hukumar Oyibo dake jihar Rivers. Tuni dai rundunar ‘yan sanda ta tabbabar da faruwar lamarin.
Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sanda DSP Nnamdi Omoni, ya ce “mun tabbatar da faruwar wannan lamarin, kuma gobarar ta tashi ne sakamakon gyaran da injiniyoyi ke yi akan bututun Mai a yankin.”
Ya ‘kara da cewa mutane da yawa sun mutu sakamakon hadarin, kuma farkon faruwar wannan lamari mutum 10 ne suka mutu, amma nan da wani dan lokaci bincike zai tabbatar da ainihin yawan wadanda suka mutu.
Sai dai kuma, a cewar wani ganau mai suna Mark Elenu, wanna lamari ya faru ne sanadiyar fasa bututun Mai da bari Mai ke yi a yankin Niger-Delta.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa akan irin asarar rayuka da aka tafka sakamakon kone-konen bututun Mai a yankin Niger-Delta, ke haddasa asarar rayuka da dinbin dukiya.
Domin Karin bayani saurari cikakken rahotan Lamido Abubakar.
Facebook Forum