Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Emirates Ya Dawo Da Zirga-Zirga A Najeriya


Jirgin saman Emirates ya kawo riga kafin coronavirus a Najeriya
Jirgin saman Emirates ya kawo riga kafin coronavirus a Najeriya

Kamfanin jiragen sama na Emirates zai ci gaba da aikin jigilar fasinjoji tsakanin Dubai da Najeriya daga ranar 5 ga watan Disamban da mu ke ciki.

Maido da aiyukan na zuwa ne bayan shafe watanni 10 da kamfanin ya dakatar da zirga-zirgar jiragen samansa zuwa Najeriya sakamakon takaddamar diflomasiya tsakanin kasashen biyu kan ka’idojin cutar COVID-19.

Kamafanin na Emirates dai ya ce zai dawo da aikin jigilan fasinjoji fasinja tsakanin Dubai da Najeriya daga ranar 5 ga Disambar shekarar 2021, tare da bai wa abokan huldarsa damar inganta hanyar zuwa Dubai.

Emirates wanda daya ne daga cikin manyan kamfanonin jiragen sama a duniya, zai ci gaba da aikin jigilar fasinjoji zuwa ko ina daga filayen tashi da saukan jiragen saman Najeriya tare da zirga-zirgar yau da kullun, yana ba matafiya daga Najeriya damar shiga Dubai, wanda ya kasance wurin shakatawa da kasuwanci sosai kamar yadda gidan talabijan na Channels ya ruwaito.

Haka kuma Emirates zai ba matafiya damar yin tafiye-tafiya daga Dubai zuwa kasashe sama da 120 a duniya.

Kamfanin Emirtates dai zai fara aiki zuwa Abuja da jiragensa samfurin EK 785 da 786 wanda samfurin EK 785 zai tashi daga Dubai da karfe 11:00 ya isa Abuja da karfe 15:40.

Kazalika jirgin da zai koma inda samfurin EK 786 zai tashi daga Abuja da misalin 19:00, ya isa Dubai da karfe 04:35 na safe a cewar kamfanin na Emirates.

Jirgin Emirates samfurin EK 783 zuwa Legas zai tashi daga Dubai da karfe 10:30 kuma ya isa Legas da karfe 15:40, in ji kamfanin.

Haka kuma, jirgin dawowar mai lamba EK 784 zai tashi daga Legas da karfe 18:10, ya isa Dubai da karfe 04:15 na safe.

A ranar 27 ga watan Nuwamban da ta gabata ne gwamnatin Najeriya ta dage haramcin da ta yiwa kamfanin jirgin saman, kamar yanda ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya bayyana.

A baya dai 'yan Najeriya sun yi ta kokawa a kan yadda haramta zirga-zirgar kamafanin Emirates ya shafe su inda 'yan kasuwa, masu neman kiwon lafiya ke bin wasu kasashe makwabta wajen tafiya da tsadar gaske in ji Auwal Mu’azu wani dan kasuwa da ya saba ruwa Dubai sayen kayayyakin da ya ke sayarsa.

XS
SM
MD
LG