Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubai Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Dage Dakatar Da Jiragen Sama Daga Najeriya


Jirgin saman Emirates.
Jirgin saman Emirates.

Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta kuma sabunta dakatar da jiragen sama da fasinjoji daga Najeriya, bayan da ta ba da sanrwar dage takunkumin.

Kwanaki 2 bayan da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta ba da sanarwar dage takunkumin hana zirga-zirgar jiragen sama da kasashen Najeriya, Afirka ta Kudu da Indiya, kasar ta kuma sauya tunani, tare da bayyana wata sabuwar dokar dakatar da shigar jiragen sama daga Legas da Abuja, daga ranar 21 ga watan nan na Yuni.

Tun a watan Fabrairun wannan shekara ne kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta dakatar da shigar jiragen sama daga Najeriya zuwa cikin Dubai, lamarin da ya sa gwamnatin Najeriya mai da martani da hana saukar jiragen kasar a Najeriya, sakamakon matsalar da aka samu ta rashin fahimta da daidaita akan hanyoyin gudanar da gwajin lafiya ga fasinjoji da ke zirga-zirga tsakanin Dubai da Najeriya.

To sai dai kamfanin sufurin jiragen saman kasar na Emirates ya ba da sanarwa a ranar Assabar, cewa zai dawo da zirga-zirgar fasinjoji daga Najeriya, daga ranar 23 ga watan nan na Yuni.

To amma kuma sai ga sabuwar sanarwa a jiya Litinin, inda kamfanin ya bayyana dakatar da daukar fasinjoji daga Legas da Abuja, da ma duk fasinjojin wasu kasashe da suka bi ta Najeriya a cikin kwanaki 14.

Sanarwar ta ba da hakuri akan duk wani cikas da matakin zai haifar, tare da yin bayanin cewa an yi ne bisa dokokin takaita zirga-zirga na kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa.

Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa har yanzu dakatarwar da aka yi wa jirage daga kasar Afirka ta Kudu tana aiki, har ya zuwa ranar 6 ga watan Yuli, bisa umarnin gwamnatin kasar na takaita shigar matafiya daga kasar ta Afirka ta Kudu zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa.

Sabon matakin na Hadaddiyar Daular Larabawa na dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga Najeriya ta haifar da cece-kuce da muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki, wadanda har sun soma farin ciki da samun sa’ida kan dage dakatarwar da aka yi wa jiragen sama da fasinjoji daga Najeriya

XS
SM
MD
LG