Gwamnatin Najeriya ta dakatar da wani kamfanin jiragen sama bisa kai mawaki Naira Marley, Abuja domin ya gudanar da wani bikin wake-wake duk da cewar an saka dokokin takaita zirga-zirga domin yaki da yaduwar cutar Coronavirus.
Ministan sufuri na kasar Hadi Sirika ne ya bayyana hakan a yayin wani taron kwamitin shugaban kasa akan cutar covid 19 da aka yi a Abuja.
Sirika ya ce jirgin wanda ya kai mawakin Abuja daga Legas, ya kamata ya dauki wani babban lauya ne mai suna Adefope Okogie.
Ya ce, "yin hakan ya keta dokoki kuma karo na biyu kenan da hakan ke faruwa, saboda haka dole mu dakatar da kamfanin na Executive Jet Services kuma zai fuskanci doka."
"Zamu kuma tuhumi matukin jirgin bisa bayar da bayanai na karya."
Mawakin ya gudanar da bikin a radar Asabar din da ta gabata a wani ginin shaguna mai suna Jabi Lake Mall da ke birnin na Abuja.
Lamarin kuma ya janyo hukumomi suka garkame ginin saboda keta dokokin da aka gindaya domin takaita cutar Covid-19.
Hakan duk na faruwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar karuwar adadin mutanen da ke kamuwa da cutar a kasar, tun bayan da aka sassauta dokokin na zama a gida.
Ya zuwa yanzu a kalla mutum 16,000 ne suka Kamu da cutar a kasar.
Facebook Forum