Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Najeriya Ta Dakatar Da Jigilar Jiragen Emirates


Jirgin saman Emirates.
Jirgin saman Emirates.

Najeriya ta dakatar da zirga-zirgar kamfanin jiragen saman Emirates zuwa cikin kasar, bayan da ya kakabawa fasinjoji ‘yan Najeriyar dokar karin matakan gwajin cutar coronavirus.

A makon da ya gabata ne kamfanin jiragen na Emirates ya ba da sanarwar cewa ya dakatar da zirga-zirga zuwa Najeriya har sai yadda hali yayi bisa umarnin gwamnatin kasar, amma bai bayar da cikakken bayani akan lamarin ba.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Hadi Sirika, ya fada a wani taron manema labarai a Abuja, cewa kamfanin ya bukaci fasinjoji daga Najeriya su gudanar da gwajin cutar coronavirus har sau 3 a cikin sa’o’i 24.

Ministan ya ce akan haka ne gwamnati ta dakatar da ayukansa a kasar, in ban da jiragen kaya da na ayukan jinkan jama’a.

Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya Hadi Sirika
Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya Hadi Sirika

Sirika ya ce “a tilasta mana yin gwaji har 3 a cikin sa’o’i 24, wannan ya wuce mizanin tunani. Tun da kuma suka dage akan haka, za’a ci gaba da dakatar da ayukansu.”

A watan da ya gabata ne ma aka dage takunkumin dakatarwa ga kamfanin na Emirates, bayan da ya bukaci karin gwajin cutar COVID-19 ga fasinjoji daga Najeriya.

Jirgin saman Emirates ya kawo riga kafin coronavirus a Najeriya
Jirgin saman Emirates ya kawo riga kafin coronavirus a Najeriya

Ko baya ga gwaji na kwa-kwaf da ake yi kafin tashin jirgin daga Najeriya, kamfanin ya kuma tilastawa fasinjoji yin karin gwaji na kai tsaye, sa’o’i 4 kafin tashin jirgi.

Sirika ya ce an sami karin wani kamfanin jiragen sama na KLM na kasar Netherlands, da ya soma zirga-zirga zuwa ciki da wajen Najeriya a wannan watan.

XS
SM
MD
LG