Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamala Harris Na Tallata Wani Shiri Na Gina Gidaje Miliyan Uku


'Yar takarar Democrat Kamala Harris
'Yar takarar Democrat Kamala Harris

Tallan yunkuri ne na jan hankalin masu kada kuri’a a jihohin da ke da muhimmanci wajen samun kuri’u wadanda suka hada da Arizona da Nevada.

Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta fitar da wani sabon talla da ke nuna wani shiri na gina sabbin gidaje miliyan 3 cikin shekaru hudu idan aka zabe ta.

Wannan mataki yunkuri ne na dakile matsalar hauhawar farashin gidaje wanda ya yi hannun riga da tsarin dan takarar jam’iyyar Republican Donald Trump.

Harris ta zayyana tsare-tsarenta cikin tallan na bidiyo mai tsawon minti daya wanda ya nuna irin rayuwar da ta fuskanta tana karama.

‘Yar takarar jam’iyyar ta Democrat ta tashi ne a gidan haya yayin da mahaifiyarta ta kwashe tsawon shekaru goma tana tara kudi kafin ta iya sayen gida.

Tallan yunkuri ne na jan hankalin masu kada kuri’a a jihohin da ke da muhimmanci wajen samun kuri’u wadanda suka hada da Arizona da Nevada.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG