Da daren jiya Laraba Tim Walz ya amince da gabatar da shi da jam’iyyarsa ta yi a matsayin wanda zai zama mataimakin shugaban kasa idan ta ci zabe. Ya yi amfani da jawabinsa ga Babban Taronn Kasa na Jam’iyyar wajen gode ma dinbin jama’a da ke dandalin saboda, abin da ya kira, “kawo farin ciki” ga yakin neman zaben da ‘yar takarar shugaban kasa, Kamala Harris ta kara wa armashi.
“Mun hallara ne da daren yau saboda wani dalili mai kyau kuma mai sauki: wato mu na kaunar wannan kasar,” a cewar Walz yayin da wasu dubban ‘yan deliget ke daga kwalaye masu dauke da sakwannin da ke cewa, “Koci Walz” da launonin ja, fari da kuma shudi.
Walz ya tabo tashinsa a Nebraska da kuma ayyukan koyarwa da horas da ‘yan wasan kwallon kafa da ya yi a Minnesota, sannan ya ce da taron jama’a, “Na gode ma ku da yadda ku ka kawo farin ciki a wannan gwawarmaya.”
“A yayin da wasu jahohi ke haramta amfani da wasu litattafai a makarantunsu, mu yinwa mu ke kawarwa daga na mu,” a cewarsa. A wani yarfe da ya yi ma takwaran karawarsa na jam’iyyar Republican, JD Vance, Walz ya kara da cewa, “Akwai yara 24 a ajin da na ke koyarwa a makarantar sakandare, kuma dukkansu babu wanda ya je Yale.”
‘Yan jam’iyyar Democrat da su ka taru a dandalin United Center da ke birnin Chicago na jahar Illinois ta Amurka, na fatan dorawa ne a kan armashin da Kamala Harris ta janyo tun bayan da ta zama ‘yar takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar a watan jiya. Su na kokarin dada karfafa kwarin gwiwar da su ka samu tun bayan janyewar da shugaba Joe Biden ya yi, a daidai lokacin da su ke kuma fitowa karara suna gaya ma magoya bayansu cewa akwai fa wata zazzafar gwagwarmaya da za su fuskanta wajen bugawa da tsohon Shugaban kasa Donald Trump.
Jawabin na Walz ya biyo bayan na tsohon Shugaban kasa Bill Clinton, wanda sake dawowa ne ya yi a wurin da ya sani sosai, wato dandanlin Babban Taron Kasa na Jam’iyyar Democrat, don caccakar Donald Trump, wanda ya kira shi mai son kansa, sannan ya yabi Kamala Harris wadda ya ce ta maida hankali kan abubuwan da Amurkawa ke muradi..
Dama dai an gayyato Clinton ne don ya kara armashi ma dare na uku na babban taron jam’iyya ta Democrat, dayake lokacin ne za a gabatar da mutumin da aka ayyana a matsayin wanda zai zama Mataimakin shugaban kasa idan jam’iyyar ta ci zabe, wato Tim Walz ga Amurkawa.
“Mu na da zabi a bayyane a gani na. Wato Kamala Harris, ta jama’a. Sannan akwai shi kuma wancan mutumin wanda ya nuna cewa, tun ba a ma yi tafiya mai nisa ba, ta kansa ya ke yi – game da ni ne, akai na ne,” a cewar Clinton.
Akwai sauran jiga jigan jam’iyyar da dama da su ka yi jawabai.
Dandalin Mu Tattauna