Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamala Harris Ta Amince Da Zabenta A Matsayin 'Yar Takarar Shugaban Kasa A Jam'iyyar Democrat


Kamala Harris yayin da ta amince da yin takara a Chicago
Kamala Harris yayin da ta amince da yin takara a Chicago

Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala harris, ta yi kira ga Amurkawa da su hada kai da a ranar Alhamis, yayin da take amincewa da zabenta da aka yi a matsayin ‘yar takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Democrat.

Ta jaddada cewa, irin yadda ta taso, da kuma gogewarta a matsayin lauya kuma mai gabatar da kara da dai sauransu, dalilai ne da suka sa ta cancanci kare muradun 'yan jam'iyyar, da kuma yin galaba kan dan takarar Republican, Donald Trump.

Da ta hau mumbari gaban dunbin jama’a, wadanda suka ta shi suna mata sawo ta yabo, a dandalin Babban Taron Kasa na Jami’iyyar Democrat a Chicago, Kamala Harris ta gabatar da kanta ga Amurkawa a hukumance, sannan ta zayyana irin tafarkin da take son kasar ta kama daga yanzu zuwa shekaru hudu masu zuwa.

Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris
Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris

Kamala Harris ta ce, “Da wannan zaben mai zuwa, kasarmu na da wata muhimmiyar dama mai matukar daraja, ta huce fushi, da nuna kyama, da gasa ta magabtaka, wadanda duk su ka faru a baya,” a cewar Harris. Ta kara da cewa, “Wata dama ce kuma, ta shata wata sabuwar hanyar mikewa. Ba a matsayin ‘yan wata jam’iyya guda ko wani bangare ba, amma a matsayin Amurkawa.”

Mahaifin Kamala Harris ya fito ne daga Jamaica yayin da mahaifyarta ta fito daga Indiya; ta kasance bakar fata ta farko, kuma mai nasaba da kudancin Asiya, da ta kai ga zama ‘yar takarar shugaban kasa ta wata babbar jam’iyya a Amurka.

Kamala Harris da Mai gidanta
Kamala Harris da Mai gidanta

Harris ta yi gargadi game da yadda Trump ya yarda da karya doka kana yake niyyar yi wa kasar rikon sakainar kashi idan aka zabe shi a wa’adi na biyu zuwa Fadar White House.

Ta ce, "Ba za mu koma baya ba" inda zauren taron ya rude da ihu yayin da Harris ta soki tarihin Trump kuma ta fara bayyana manufofinta ga al'ummar kasar.

Dimbin magoya bayan jami'iyar Democrat a Chicago
Dimbin magoya bayan jami'iyar Democrat a Chicago

"Muna tsara wata sabuwar hanya ta yin gaba, gaba zuwa gaba tare da masu matsakaicin karfi," in ji Harris. "Kuma gina wannan al’ummar ta matsakaicin karfi shi ne makasudin shugabancina."

Idan aka zabe ta, za ta zama mace ta farko da ta zama shugabar Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG