Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

 ‘Yan Deliget Sun Kada Kuri’ar Tabbatar da Takarar Kamala Harris


Democratic National Convention (DNC) in Chicago
Democratic National Convention (DNC) in Chicago

A daren jiya an shiga babi na farko na daya daga cikin rukunoni mafiya muhimmanci na wannan taron, wato kiran ‘yan deliget daga jihohin Amurka, su yi shelar kada kuri’unsu ga ‘yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta Democrat, Mataimakiyar Shugaban kasa, Kamala Harris.

Bayan da aka yi hidimomi da harkokin da aka saba yi tun bayan bude babban taron jam’iyyar Democrat da daren shekaran jiya Litini, kamar kade kade da raye raye, da kuma jawabai daga wasu kusoshin jam’iyyar ta Democrat, a daren jiya an shiga babi na farko na daya daga cikin rukunoni mafiya muhimmanci na wannan taron, wato kiran ‘yan deliget daga jihohin Amurka, su yi shelar kada kuri’unsu ga ‘yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta Democrat, Mataimakiyar Shugaban kasa, Kamala Harris.

Sakataren wannan babi na taron ya yi ta gayyatar jahohi, daya bayan daya, su na hawa kan mumbari su na shelar yadda za su kada kuri’arsu. Alal misali, Sakataren ya ce “ya ke jahar Mississippi, yaya za ki kada kuri’arki yau,” inda shi kuma wakili ko deliget na jihar, ya amsa, ya hau kan mumbari, ya yi koda jaharsa, da shahararren kogin nan na Mississippi, tare da zayyana irin shahararrun mutanen da su ka fito daga jahar, sannan ya ce, “Ya Sakatare, cikin matukar farin ciki, jihar Mississippi na mai kada kuri’u 40 ga shugabar kasarmu ta gaba, Kamala Harris.”

Former US President Barack Obama (L) greets Former US First Lady Michelle Obama on the second day of the Democratic National Convention (DNC) at the United Center in Chicago, Illinois, on August 20, 2024.
Former US President Barack Obama (L) greets Former US First Lady Michelle Obama on the second day of the Democratic National Convention (DNC) at the United Center in Chicago, Illinois, on August 20, 2024.

Daga nan sai kuma aka sake shiga babin sauraren jawaban kusoshin jam’iyyar, ciki har da Sanata Bernie Sanders da Shugaban Majalisar Dattawa, Chuck Schumer, wadanda duk su ka caccaki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican, Donald Trump, tare da tallata gwanarsu.

To amma, kamar yadda aka zata, lokacin da aka gayyato Matar tsohon Shugaban Amurka Barak Obama, wato Michelle Obama, wanda hakan ke nufin sharar fage ga zuwan Obama kansa, sai taron ya game da sowa ta yabo. Mechelle Obama ta ce, “Akwai wani abun al’ajibi da ke yawo a sama. Ko ba haka ba? Mu na jinsa a wannan dandalin, amma ya na bazuwa a fadin wannan kasa da mu ke kauna. Wani abu ne da mu ka saba ji; kun san abin da na ke nufi: Wato tasirin karfin gwiwa, wanda ke yaduwa, Ta ce “yanzu an samu wata dama kuma ta kawar da iblisanci na tsaro, da raba kawunan jama’a da kuma tsanar juna wadanda su ka dabaibaye mu, kuma sun ci gaba da dabaibaye mu ya yin da mu ke kokarin cimma abubuwan da iyayenmu su ka sadaukar da rawukansu a kai.”

Democratic National Convention (DNC) in Chicago
Democratic National Convention (DNC) in Chicago

Shi kuwa tsohon Shugaban kasa, Barack Obama, da ya hau kan mumbarin, ya tabo batutuwa da yawa, ya kuma jinjina ma shugaba mai ci, Joe Biden. Ya ce manufofin da aka ginu a kai cikin shekaru hudu da su ka gabata su ne Amurka ke bukata. “A daidai lokacin da miliyoyin mutane ke mutuwa, ana bukatar shugaban da ba zai siyasantar da al’amura ba” Obama ya soki yadda, a cewarsa, jam’iyyar Republican ta zama damkar mallakar wani mutum guda, wato Trump.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG