MINNA, NIGERIA - Ko baya ga matsalar tsadar rayuwa a yanzu, matsalar rashin tsaron da ya addabi sassan Najeriya na zama kalubale ga manema labaran kasar musamman idan aka yi la’akari da irin kiki-kaka da ake samu a tsakaninsu da hukumomin kasar wajan samun sahihan bayanai da ya kamata a baiwa al’umma da zai taimaka wajan kwantar da hankalinsu.
A wani babban taro na makon ‘yan jaridu da ya gudana a jihar Neja, an gabatar da jawabai tare da karawa manema labaran kwarin guiwa akan aikinsu na taimakon ‘yan kasa.
Sakataren Kungiyar ‘Yan Jaridu ta NUJ a jihar Neja, Kwamred Usman Chiji yace babban taron ya nuna bukatar kulawa ta musamman ga ‘yan jaridu na jihar da kuma kasa baki daya.
To amma neman hanyoyin shawo kan matsalolin da suka addabi Najeriya shine ya dauki hankalin wasu ‘yan jaridu da suka halarci taron.
Gwamnatin Najeriya dai ta ce tana kokarin shawo kan matsalolin da ‘yan kasar suke fuskata.
Ministan labaran Najeriya Muhammad Idris Malagi wanda babban daraktan gidan rediyon Muryar Najeriya, Jibrin Baba Ndache, ya wakilta a wannan taro ya nuna bukatar ganin ‘yan jaridun sun maida hankali wajen wayar da kan ‘yan kasa duk kuwa da kalubalen da suke fuskanta.
Da dama daga cikin ‘yan jaridu na samun kansu cikin hali na barazana daga bangarorin jama’a ko ma na gwamnati a kasar, a kokarinsu na yin aikinsu kamar yadda doka ta tanada.
Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:
Dandalin Mu Tattauna