Shirin tabbatar da kwarewa a aikin 'yan jarida don babban zaben 2024, wanda kungiyar ‘yan jarida ta Ghana da ofishin jakadancin Amurka a Ghana suka kaddamar mai lakabin: "Yan Jarida domin Tattaunawar zaman Lafiya" na tsawon watanni 10, zai ba da damar kiyaye ka'idojin 'yancin 'yan jarida, da inganta kwarewar aiki, tare da ba da gudummuwa wajen hana tashin hankali da kuma tabbatar da sahihin zabe, da zaman lafiya kafin zaben, a lokacinsa, da kuma bayansa.
A jawabinsa wajen taron kaddamar da shirin da aka yi a Accra, shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Ghana, Albert Kwabena Dwumfour, ya gode wa ofishin jakadancin Amurka a Ghana bisa gagarumin goyon bayan da yake bai wa ‘yan jarida.
"Yancin fadin albarkacin baki ba yana nufin barin mutane su yi ta magana kawai ba, har ma da tabbatar da alhakin gudanar da aiki yadda ya kamata," a cewar Dwumfour. "Sakamakon binciken da kungiyar GJA/MNC ta gudanar a kafafen yada labarai a lokacin zaben 7 ga watan Disamba, ya nuna cewa harzuka mutane a kafafen yada labarai ya fi yawan tashe-tashen hankula da aka tafka a lokacin zaben. Ina son nanata cewa kungiyar GJA ba ta yarda kuma ba za ta lamunci rashin da'a ba. Ba za mu ba da kariya ga wadanda suka karya doka ko nuna rashin kwarewa ba,” in ji shi.
A madadin ofishin jakadancin Amurka, shugaban sashen kafafen yada labarai, Kevin Brosnahen, ya jaddada muhimmancin kwarewa a aikin jarida wajen gudanar da zabe cikin lumana, ya kuma yi alkawarin tallafi daga ofishin jakadancin don horar da 'yan jarida.
"Za mu goyi bayan horon da kungiyar GJA za ta bayar ga ’yan jarida don inganta rahotannin gaskiya game da zabe, da taimakawa wajen yaki da yada labaran karya na zabe, da ba da kwarin gwiwa wajen yada ingantattun bayanai dake da alaka da zabe, a cewar Brosnahen.
Alhaji Osman Garba, dan jaridar gidan talabijin na kasa (GTV), a tsokacinsa ga Muryar Amurka ya bayyana muhimmancin bambanta labaran gaskiya da na karya. Ya kuma ce lallai samun kayan aiki na zamani da horo kamar wannan zasu taimaka kwarai.
“Ta hanyar ‘yan jarida ake samun labarin abin da ke wakana a wajen zabe, a saboda haka idan ba a kawo labaran da suka dace ba, lamarin zai baci. Lallai wannan horon na da muhimmanci kwarai da gaske,” a cewar Alhaji Garba.
Wani dan jarida dake Amanie FM mai suna Abbas Ayyub Babaguni, ya yaba da wannan mataki da kungiyar GJA ta dauka na ba da wannan horo ga ‘yan jarida, ya ce duba da Irin rikice-rikicen da ake samu sanadiyar yada labaran karya a lokutan zabe.
Taron ba da horon dai ya samu halartar wakilin hukumar zabe ta kasa, da hukumar 'yan sanda ta Ghana, da majalisar zaman lafiya ta kasa, da wakilan manyan jam'iyyun siyasa biyu a Ghana wato NPP da NDC, kuma duka a jawabansu sun yi alkawarin bayar da goyon baya ga wannan shiri.
Saurari rahoton Idris Abdullah:
Dandalin Mu Tattauna