Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Yi Baya Mafi Muni Cikin Shekaru 18 A Kididdigar ‘Yancin ‘Yan Jarida


Jaridun kasar Ghana
Jaridun kasar Ghana

A shekara ta biyu jere, kasar Ghana ta sake faduwa a kididdigar ‘yancin ‘yan jarida ta shekara-shekara da kungiyar Reporters without Borders (RSF) ta fitar a ranar Laraba, ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya.

Wannan shi ne mafi muni matsayin Ghana cikin shekaru 18, tun bayan da ta taba kai matsayi na 66 a shekarar 2005. Ghana ta sauka daga matsayi na 60 a bara zuwa na 62 a wannan shekara ta 2023. Sai dai a tsakanin kasashen Afirka, Ghana ta zo matsayi na 9, inda ta dara daga matsayi na 10 a rahoton shekarar 2022.

Kasar Namibia ce ta farko a Afirka, sai kasashen Africa ta kudu, Cape Verde, Seychelles, Gambia, Ivory Coast, Burkina Faso da Niger na biye, sannan Ghana. Kasar Najeriya ta haura matsayi shida fiye da na bara, daga matsayi na 129 zuwa 123; Kamaru ta fado mataki 20, zuwa matsayi na 138 daga kasashe 180 a duniya.

A cewar kididdigar, 'yan jarida na fuskantar matukar wahala wajen gudanar da aikinsu a kusan kashi 40 cikin dari na kasashen Afirka, idan aka kwatanta da kashi 33 cikin dari na bara.

'Yancin 'Yan Jaridu
'Yancin 'Yan Jaridu

Muryar Amurka ta yi hira da wandasu 'yan jarida a kasar Ghana dangane da wannan rahoto wadanda su ka bayyana matsalolin da 'yan jarida ke fuskanta a kasar da suka janyo wannan koma bayan.

A bayaninsa, Abdallah Sham’un Bako, wakilin gidan rediyon RFI a Ghana ya ce, ‘yan jarida na fuskantar barazana da cin zarafi idan ya fitar da bayanai da suka shafi wasu, musamman ‘yan siyasa. Yace, ya kamata a yi duba a daina hakan.

Ita kuwa Maryam Bawa ta gidan rediyon Marhaba dake Accra ta ce, matsalar mata da suke aikin jarida a Ghana suke fuskanta ta wuce misali, domin akwai wasu wuraren ma da ba su iya shiga su gudanar da aikinsu domin tsoron rayuwarsu. Ta ce, abin takaicin ma, a duk lokacin wani taron manema labarai ko wani dan siyasa ke gudanar da taro, suna nunawa cewa za su kare hakkin ‘yan jarida, amma akasin haka ne ke faruwa.

Wata 'yar Jarida a kasar Kamaru
Wata 'yar Jarida a kasar Kamaru

A nasa bangaren, Abdul-Wahab Jawando na Gaskia TV, cewa ya yi, “ba za mu ce ba mu da ‘yanci sam sam ba, muna da ‘yancinmu amma akwai matsala”. Yace, akwai wasu ‘yan jarida da aka yi musu lahani, har yanzu ana bincike, lokaci mai tsawo ba a kammala ba. Kuma duk da yake dokar ‘yancin samun labarai na nan, amma ‘yan jarida na wahala kafin su samu bayanai da suke bukata.

Fitaccen dan jarida mai binciken kwakwaf a Ghana, Manasseh Azure, ya baiwa gwamnati shawara. Yace: “Kira na ga Shugaban kasa, Ministan yada labarai da Gwamnatin Ghana, ku daina karyata rahotanin 'yan jarida, hatsarin gaske ne”. Ya bayyana cewa, a shekarar 2017 ya ba da rahoton barazanar kisa a kaisa da yawa ga hedkwatar 'yan sanda kuma babu abin da aka yi a kai, tilas ya sa ya bar kasar a lokuta biyu domin ya tserar da ransa. Bisa ga cewarsa, ya san wasu 'yan jarida da suka shiga masifa a cikin wadannan lokutan. Ya kuma yi kira ga shugaban kasa ya tashi tsaye, kuma ya saurari korafe-korafen 'yan jarida.

Ghana ta taba kai matsayi na 22 a duniya a shekarar 2015. A shekarar 2018, kasar ta kasance ta daya a Afirka kuma ta 23 a duniya.

Saurari cikakken rahoton Idriss Abdullah cikin sauti:

Koma Bayan 'Yancin 'Yan Jarida a Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG