Shugaban na Faransa ya kara da cewa sabon salon da gwamnatinsa ta bullo da shi a huldar ayyukan tsaro na hangen girke dakaru a wasu kasashen Afirka ciki har da Najeriya.
Shugaba Macron da ya ke jawabi wa jakadun kasar a taron ta ya yi murnar shiga sabuwar shekara a jiya Litinin 6 ga watan Janairun 2025, da cewa mu muka bai wa shugabanin kasashen Afirka shawarar sake fasalta zaman sojanmu a nahiyar.
Saboda mu masu da’a ne muka ba su damar su fada a fara ji daga bakinsu.
Ba dan mun yi shuru ba, za a juya magana ana cewa an kore mu daga Afirka.
Emmanuel Macron ya ci gaba da cewa: “Za mu sake bude wani sabon babi a yarjejeniyar tsaro ta hanyar kafa sansanonin musamman, mu kuma kara wa sansanin Djibouti karfi. Za mu bukaci abokan hulda su bayyana abin da suka fi bukata a wannan fanni. Za kuma mu fi maida hankali kan bada horo da kayan aiki da samar da bayanan sirri, mu kuma duba ka’idodin yarjeniyoyi sannan mu tantance girman barazanar da za a tunkara kamar yadda muka yi a ‘yan shekarun nan da Benin wacce ba a taba samun irin ta ba, haka kuma muna da niyyar kulla irin wannan yarjejeniya da Najeriya.”
Wadanan kalamai na shugaban Faransa sun dauki hankulan jama’a a jamhuriyar Nijar inda ‘yan kasar ke cewa gaskiya ce ta yi halinta.
Emmanuel Macron ya kara da cewa: “Ina gaya wa shugabanin Afirka wadanda suka gaza gaya wa al’umominsu gaskiyar lamari in ba don Faransa ta girke sojojinta ba to sam da ba za su yi shugabancin wata kasa mai ‘yancin kanta ba.”
Chadi da Senegal wadanda a yanzu ayyukan ficewar sojan Faransa ke gudana sun yi tir da jin kalaman na shugaban Faransa.
Inda ministan harkokin wajen Chadi Abderamane Koullamala a sanawar da ya fitar ya bayyana cewa tallafin Faransa ga sojojin Chadi bai taka kara ya karya ba. Jarumtar dakarun tsaron Chadin wani abu ne da ya samo asali daga jajircewar al’ummarta.
Shi kuwa Firaiministan Senegal Ousmane Sonko ya jaddada cewa ficewar sojan Faransa wani mataki ne da Senegal ta dauka a matsayinta na kasa mai ‘yancin kanta. Ba inda aka yi wata shawara ko batun sulhu da Faransa, saboda haka maganganun shugaba Macron ba su da tushe.
Faransa wacce ta fara girke dakaru a shekarar 2013 a Mali na fuskantar turjiya a kasashen Sahel tun daga shekarar 2022 inda jama’ar Mali da Burkina faso da Nijar suka kori dubban sojojin da ta girke da sunan yaki da ta’addanci.
Al’amarin mai kama da annoba ya afkawa dakarun Faransar da ke Chadi kamar yadda a farkon watan nan na Janairu Senegal da Cote d’ivoire suka bi sahu.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna