A yayin wata tattaunawa da shugaban kasar Faransa Emanuel Macron yayi da takwaran aikinsa na kasar Ivory Coast Alassane Ouatara ne ya bayyana fatan tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar a watan Yuli, bisa sharadin sai sun saki hambararren shugaban kasa Bazoum Mohamed.
Shugaban na Faransa da na Ivory Coast sun tattauna kan halin da tsaro ke ciki a yankin Sahel da kuma batun juyin mulki a Nijar da ke neman kawo rarrabuwar kawuna a yankin yammancin Afrika, a yayin wata ganawa da suka yi a birnin Paris.
Dangantaka tsakanin Nijar da Faransa, wacce ta yi wa Nijar din mulkin mallaka ta yi tsami tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar, wanda gwamanatin Faransa ta ki amincewa da sojojin.
To sai dai masana na ganin kalaman na shugaba Macron na nuni da cewa kasar ta Faransa ta sassauto daga matsayarta a kan sabbin mahukuntan Nijar sakamakon yadda suka juya mata baya ta hanyar neman sabbin kasashen da Nijar zata yi hulda da su.
Abdourahamane Dikko, masanin harkokin yau da kullun ne a Nijar, ya ce salon da kasar Faransa ta bullo da shi abin dubawa ne.
Macron dai ya jaddada goyan bayansa ga matakin kasashen yammacin Afrika tare da shan alwashin nemo mafita kan halin da Nijar ke ciki, sai dai masana sun bukaci mahukuntan Nijar su yi taka-tsantsan da Faransa, da suke ganin tana shirya wata makarkashiya a kan Nijar.
Kungiyar kasashen yammancin Afrika ta ECOWAS, dai ta kakaba wa Nijar takunkumi mai tsanani tare da barazanar amfani da karfin soji wajen dawo da tsarin mulkin farar hula a kasar, idan har suka kasa samun jituwa da shugabannin mulkin sojojin, ita ma kasar Ivory Coast ta ce a shirye take ta tura bataliyar sojojinta.
Saurari rahoton Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna