Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Juyin Mulkin Nijar: Rana Ta Biyu A Taron Hafsoshin Sojin Kasashen ECOWAS


Lokacin taron Rundunar Sojojin ECOWAS na kwana biyu a Accra, Ghana
Lokacin taron Rundunar Sojojin ECOWAS na kwana biyu a Accra, Ghana

A yau Juma’a hafsoshin sojojin kasashen yammacin Afirka suke zaman tattaunawa a rana ta biyu kuma ta karshe a birnin Accra, na Ghana, inda suka yi ta tofa albarkacin bakinsu kan yiwuwar amfani da karfin soja a Nijar, idan har tsarin diflomasiyya ya kasa kawo karshen juyin mulkin da sojoji suka yi.

WASHINGTON, D. C. - A ranar 26 ga watan Yuli ne dai jami’an soji suka hambarar da zababben Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum, kuma suka yi fatali da kiraye-kirayen da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar ECOWAS ta Afirka ta Yamma da sauran su suka yi na a maido da shi bakin aiki, lamarin da ya sa kasashen yankin suka ba da umurnin cewa dakarunsu su zauna cikin shiri.

Wasu daga cikin Rundunar Sojojin ECOWAS lokacin da suka je taron gaggawa na kwana biyu a Accra, Ghana
Wasu daga cikin Rundunar Sojojin ECOWAS lokacin da suka je taron gaggawa na kwana biyu a Accra, Ghana

A yayin ganawar tasu ta kwanaki biyu, wacce aka kammala da bikin rufewa daga misalin karfe 1600 agogon GMT, hafsoshin tsaron sun tattauna kan dabaru da sauran abubuwan da za a iya turawa, kamar yadda jadawalin hukuma ya nuna.

Har yanzu dai amfani da karfin soji ya kasance mataki na karshe, amma “idan komai ya gaza, jaruman kasashen yammacin Afirka, a shirye suke su amsa kiran aiki,” in ji kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS Abdel-Fatau Musah, a farkon taron a ranar Alhamis.

Manyan Hafsoshin Kungiyar ECOWAS Sun Fara Gudanar Da Taron Wuni Biyu A Ghana
Manyan Hafsoshin Kungiyar ECOWAS Sun Fara Gudanar Da Taron Wuni Biyu A Ghana

Ya ce akasarin kasashe 15 na kungiyar a shirye suke su shiga cikin rundunar tsaron ko-ta-kwana, in ban da wadanda suke karkashin mulkin soja, na Mali, Burkina Faso da Guinea da kuma karamar kasar Cape Verde.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG