Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Joseph Kabila Ya Lashe Zaben Kwango

Shugaba Joseph Kabila na Kwango yake kada kuri'arsa.
Shugaba Joseph Kabila na Kwango yake kada kuri'arsa.

Hukumomin Zabe a Kwango sun ayyana shugaban kasar Joseph Kabila, a matsayin mutuminda ya lashe zaben kasar, amma babban abokin hamayyarsa yayi watsi da sakamakon zaben, ya kuma ayyana kansa shugaban kasar kwango.

Yau Jumma’a ce hukumar zaben kasar ta saki sakamakon zabe na karshe, tana cewa Mr. Kabila ya sami kashi 49 cikin dari na kuri’u da aka kada, da haka ya doke dan hamayya Etienne Tshisekedi, wadda hukumar tace ya sami kashi 32 cikin dari na kuri’un da aka kada , san nan wasu ‘yan takara suna biye a baya.

Nan da nan, dan hamayya Mr.Tshisekedi, ya gayawa Sashen Faransa na Muriyar Amurka cewa, yana kallon sakamakon zaben a matsayin “takala”. Yace yana kallon kansa daga yau a matsayin shugaban kasar Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango mai jiran gado”.

Wani dan takarar shugaban kasa, Vital Kamhe, ya gayawa Sashen Faransa na Muriyar Amurka cewa, ya hakikance cewa Mr. Tshisekedi ne shugaban kasar jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango.

Jamhuriyar dake mulkin kasar, tace shugaba Kabila ne ya lashe zaben kuma da adalci, kuma duk wani wadda yake da ja kan haka ya tafi kotu.

Bayan an bayyana sakamakon zaben, wakilin Muriyar Amurka ya bada labarin ganin ana kona tayoyi a unguwannin da dan hamayya Tshisekedi yake da goyon baya, amma babu alamun wani gangamin masu zanga zanga mai girma kan sakamakon zaben.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG